September 18, 2026

Babbar Sallah: Minista Matawalle Yaraba Raguna 3000 A Zamfara

FB_IMG_1749110046203

Babbar Sallah: Minista Matawalle Yaraba Raguna 3000 A Zamfar

Daga Hussaini Yero

Tsohon gwaman Jihar Zamfara,Kuma Ƙaramin ministan tsaro na ƙasa Hon. Bello Muhammad Matawalle ya raba raguna 3000 ga jama’a da kuma ‘yan jam’iyyar APC domin yin Layya na bukukuwan salla a Jihar Zamfara.

Da yake jawabi ga manema labarai, yayin rabon ragunan a Gusau yau Laraba, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Tukur Ɗanfulani ya bayyana cewa, za a bai wa shugabannin jam’iyyar na ƙananan hukumomi rago 1400 a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar.

“Ya ci gaba da cewa, za a bai wa manyan ‘yan kwamitin Zartarwar na jam’iyyar na jiha da na ƙananan hukumomin APC da dattawa da matasa da malaman addini raguna 1600.zasu amfana da su.

Tukur Dan Fulani, ya yabawa minista Matawalle bisa wannan karimcin, sannan kuma ya buƙaci waɗanda suka amfana da ragunan dasu yi amfani da raguna a matsayin Layya a lokacin Sallah kamar yadda Allah Ta’ala ya tsara.

Kuma ya yabawa Sanata Abdul’aziz Yari da Muktar Koguna akatan kokarin su na bada tallafi Shanu da ragunan Layya.

Ya kuma bayyana cewa, APC za ta dawo da mulki a 2027 a Jihar Zamfara.

About The Author