September 17, 2026

Hukumar Hisba Ta Yaba Da Ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Katsina ga Mahajjatan Bana. 

IMG-20250607-WA0021

Hukumar Hisba Ta Yaba Da Ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Katsina ga Mahajjatan Bana.

Hukumar Hisba ta jihar Katsina ta yaba da namijin ƙoƙarin da gwamnatin jihar Katsina ta yi ƙarƙashin gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa akan alhazan bana a ƙasa mai tsarki.

Mataimakin shugaban kwamandan na jiha Dakta Ibrahim Iyal Gafai ne ya bayyana haka a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da kafar sadarwa ta Popular News.

Dakta Ibrahim ya bayyana cewa saɗaukarwar da amirul Hajj na bana Mataimakin gwamna Malam Faruq Lawal Jobe ya nuna abin a yaba ne, musamman irin yadda ya riƙa tsayawa duk abinda za a yi wa alhazai daga jihar Katsina ya kasance abu ne mai kyau.

” Irin yadda Malam Faruk Lawal Jobe ya riƙa yi a Minna musamman wajen abincin alhazai, sannan wani abin birgewa da ban sha’awa shi ne, yadda yake mu’amala da kowa da kowa ba tare da nuna cewa shi wani ba, wannan shi ne irin sa na farko da wani shugaba ya ƙasƙantar da kansa wajen yi wa Allah da al’umma hidima” inji Dakta Ibrahim

Ya kuma ƙara da cewa, a iya sanin sa, babu wata matsala da ta shafi alhazan jihar Katsina wanda mataimakin gwamna ya yi magana ba a magance ba ta.

Mataimakin kwamandan Hisba ya ƙara cewa dole idan mutum ya yi abinda ya kamata a yaba masa domin a karfafi gwiwar saura su yi koyi da shi musamman abinda ya shafi al’umma.

A cewar sa, gwamnatin jihar Katsina ta cancanci a yaba mata a bisa wannan namijin ƙoƙari da aka yi wajen ganin alhazzai jihar Katsina sun sha bamban da sauran alhazai tare da irin kulawar da suka samu a ƙasa mai tsarki

Haka kuma ya ƙara da cewa hatta malamai da aka taho da su daga jihar Katsina domin su ilmantar da jama’a, an yi abinda ya da ce saboda yawan su da sauran ma’aikata da gwamnati ta ɗauka nauyi domin ganin an samu nasara a wannan aiki Hajj na bana.

Dakta Ibrahim Iya Gafai ya bayyana cewa irin yadda gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa ya riƙa nunawa mahajjata daga jihar Katsina abin birgewa ne musamman yadda ya riƙa nuna cewa shima mutum kamar kowane Alhaji.

Daga ƙarshe ya yi kira ga mahajjatan da su cigaba da sanya jihar Katsina cikin addu’o’in su da kuma gwamnatin jihar Katsina domin samun nasarar matsalar tsaro da ake fama da ita

Haka kuma ya addu’ar Allah ta’ala ya karbi ibadunmun mahajjatan jihar Katsina da Nijeriya da kuma duniya baki daya.

About The Author