Asibitin Koyarwa Katsina: Miliyan 70 Muke Biya Kudin Wuta Duk Wata Dole Tasa Muke Cajin Marasa Lafiya -MD
Asibitin Koyarwa Katsina: Miliyan 70 Muke Biya Kudin Wuta Duk Wata Dole Tasa Muke Cajin Marasa Lafiya -MD
Shugaban asibitin koyarwa na Katsina Dakta Bello Sulaima Muhammad ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai akan wasu zarge-zarge da ake yi shugabancin asibitin.
Dakta Bello Sulemain ya bayyana cewa idan kana biyan kuɗin wuta naira miliyan 70 duk wata komi ya durkushe ke nan, saboda yanayin da aka shiga yanzu ba mai jin dadin yadda yake tafiyar da aiki shi.
Shugaban Asibitin koyarwar yaa ƙara da cewa lokacin da aka samu matsalar wuta a arewacin Nijeriya duk kwana biyu, sai ya sayi litar Gas 3,000 akan kuɗi naira miliyan 3 da dubu ɗari 6 ga shi kuma an ɗauki lokaci wutar bata dawo ba.
A cewar Dakta Bello Sulemain ko lokacin da aka samu matsalar wuta, asibitin bai daina aiki ba, kodayaushe akwai wuta, dole a gudanar da wannan asibiti sannan dole a caji marasa lafiya domin a gudanar da asibitin kamar yadda aka saba.
“Sannan idan har Nijeriya bata yi maganin matsalar wutar lantarki ba, to a manta da batun cigaba, saboda komi ya koma sai an yi amfani da wuta musamman a tsarin fasahar asibitocin zamani da ake amfani da shi yanzu’
Dangane da zargin ana azabtar da jama’a musamman waɗanda suke zuwa daga karkara wajen biyan wasu kuɗadai kafin a duba marasa lafiyar su, inda suke shan wahala kafin kuɗaɗan su su dawo bayan an sallami marar lafiya ko Allah ya yi masa rasuwa.
Dakta Bello ya kare kansa da cewa tsarin asibitin ne haka, kuma ya ƙara da cewa akwai tsarin da ake bi wajen karɓar kuɗaɗan da mutum ya rage a asusun ajiyar sa (wallet) kuma tsarin yana aiki.
Kazalika akwai zarge-zarge da ake yi wannan asibiti wanda ya haɗa da zargin jingine kashiyoyin asibitin koyarwar inda aka maye gurbin su da wasu kamfanoni P.O.S domin su cigaba da aikin amsar kuɗi.
To, sai dai, shugaban asibitin koyarwa ya yi ƙarin haske akan wannan batu inda ya ce “baban dalilin da ya sanya muka jingine kashiyoyin mu gefe guda saboda rashin maida hankali, an zo aiki da safe kashiya baya nan, da rana ya tafi ɗaukar yara makaranta, ranakun ƙarshen mako bai zo aiki ba, sau nawa ake bugu waya cewa ga wuri nan da marasa lafiya, muna da kashiya guda 7 amma ko ɗaya bai zo aiki ba.”
An kuma zargin shugaban asibitin koyarwa da cewa kamfanin matarsa ne ya kawo domin yin wancan aiki na karɓar kuɗaɗai a hannun marasa lafiya maimakon kashiyoyin asibitin.
Dakta Bello Sulemain ya kare kansa da cewa “Idan har na kawo kamfanin matata domin su yi aiki, na zama wanda bai san abinda yake ba, ke nan, an kawo kamfanin ne domin ya sauƙaƙa ayyuka amma ba don wani abu ba”
Kazalika ya zargi kashiyoyin da ke aiki a asibitin koyarwa da cewa sun riƙa riƙe canjin al’umma inda wani na iya tara Naira 10 zuwa 20 a rana na canji mutane, amma yanzu da suka kawo kamfanin P.O.S wannan harƙalla ta wuce.
Dangane da batun kokawa da al’umma ke yi na cewa adadin iskar oxygen din ake ba su bai kai na kuɗin da suke biya ba, ya amsa da cewa sai dai wajen sanya shi ga marar lafiya ake samun matsala, ko a ce gwangwanin bai cika ba, ko yana zuba, ko kuwa wanda ke sayawa bai da ƙwarewa.
Ya ƙara da cewa a asibitin koyarwa na Katsina ba sa cajin marar lafiya kuɗin Iskar Oxygen saboda yanayin da al’umma suke ciki, sannan ya bayyana cewa a bincika sauran jahohi a ji abinda marasa lafiya ke biya akan kowace lita ta ‘Oxygen’
A cewar sa, saboda sauƙin da iskar oxygen ɗin su yake da shi yasa daga wajen asibitin ake zuwa saye, ya ƙara da cewa abinda zai yi maganin masu korafi shine su dakatar da sayen iskar oxygen a asibitin koyarwa ta Katsina
