September 17, 2026

APC Na Iya Faɗuwa Zaɓen 2023 A Dalilin San Rai Wajan Ɗaukar Mataimakin Ɗan Takarar Dikko Raɗɗa.

0

Sako Daga Matasa Masoyan Jam’iyyar APC Katsina

Sanin kowa ne jihar Katsina tana fama da matsalar tsaro, wanda yaa Kamata Ace Dan Takarar Gwamna Ko Mataimakin Dan Takarar Gwamna ya Kasance Akwai Asanin Tsaro Wanda Zai Iya Ba Jam’iyyar APC Nasara Wajan Samun Nasara Ga Masu Jefa Kuri’a Saboda Ganin Wanda Zai Iya Kawo Masu Nasara Wajan Yakar Yan Ta’adda Da suka Addabi Jahar Da Kasa Baki Ɗaya

Daga Ranar Da Aka Ce Faruk Lawal Jobe Ne Mataimakin Dan Takarar Gwamna Jam’iyyar APC ta fada Shakku Ga Talakawan Jahar Da Yan Jam’iyyar, Hakan Ya sanya Masoya Jam’iyyar Suka Fidda Rai A Zaban 2023 musamman Matasan Yan Gwagwarmayar Daga Kowace Karamar Hukuma Da Duka Haɗa Da Batsari, Safana , Danmusa, Kankara, Jibia, Charanci, Funtua, Kurf, Kaita Da Sauransu.

Wannan Yasa Matasa Yan Gwagwarmayar suke Kira ga Maigirma Gwamna Alhaji Aminu Bello Masari tare Da Dr. Dikko Umar Raɗɗa da Dukkan Masu Ruwa Da Tsaki Na Jahar Da Su dubi Girman Allah Su Duba Chancantar Alhaji Abdulkareem Dauda Tsohon AIG Su bashi Mataimakin Dan Takarar Gwamna Dan Sanin Tsaro Da Iya Kawo Karshen Dukkan Yan Ta’adda a Jahar Katsina Dama jahohi Makwaftan Mu

AIG Abdulkareem Dauda Masani Ne Akan Tsaro Na Zamani Da Sauransu, Wannan Bawan Allan Yayi Fice Wajan Sanin Makamar Aikin Dan Sanda Shiyasa Shugaban Yan sanda Na DUNIYA Ya Zabeshi Cikin Yan sandan DUNIYA Yanzu Haka Yana Aiki Dasu Kusan Kasashe Goma Yake Aiki Yanzu Haka Daga Lokacin Da Ya Fadi Zaben Fidda Gwani.

Muna Kira Ga Gwamnatin Najeriya Da Gwamnatin Jahar Katsina Tare Da Uwar Jam’iyya Da Sarakunan Najeriya Su fito Su Ceci Jahar Katsina Su bada Shawara Ga Dr. Dikko Umar Radda da Gwamna Masari Dan Allah Suba Abdulkareem Dauda Mataimakin Dan Takarar Gwamna Saboda Ganin Ba Muda Damuwar Da Ta wuce Tsaro Ga kuma Masanin Tsaro Cikin Jahar Katsina Daga Shiryar Daura.

Shawarar Matasan Jahar Katsina Idan Muka Dawo Maganar Siyasa Kaf Babu Wanda Yafi Alhaji Abdulkareem Dauda Cancantar Zama Mataimakin Gwamna Duba Da Yanda Yake Kishin Jahar da Jam’iyyar APC, Abdulkareem Dauda Yafi Dikkan Yan Jam’iyyar APC Cancantar Zama Mataimakin Dan Takarar Gwamna Indai Nasarar Cin Zabe Muke Tare Da Adalci Wajan Karba Karba, 2023 Bai Dace Muyi Watsi Da Al’ummar Yankin Daura Ba, Ba Su Da Dan Takarar Gwamna Yaci Ace Suke da Dan Takarar Mataimakin Gwamna Dan Naman Hadin Kan Jahar Da Nuna Kauna Ga Daurawa

Ya Allah Kataimaki Najeriya

Ya Allah Kaba Jahar Katsina Zaman Lafiya.

Sakon Matasa Masoya Nasarar Jam’iyyar APC Katsina

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *