September 16, 2026

Anyi Kira Ga Gwamnantin jihar Katsina Da Ta Dubin Wannan Wurin Da Idon Rahama

0

Jaridar SRTV ta ruwaito hadururruka kan farune adalili da lalacewar hanyoyi wani sa’ilin kuma rashin kyakkyawar kulawar direbobi ke haddasa asarar rayuka da kuma dukiyoyi.

A wannan karon al’mmomi ne da suka hada da direbobi da matafiya suka koka da irin lakacewar da wannan wuri da ke mutukar muhimancin gaske musanman ga masu Kai kawo a tsakanin gàrin Katsina zuwa Marabar Kankara.

Kasantuwar wannan wuri mahada ce ta hanyoyin da suka taso daga Katsina zuwa Marabar Kankara da Kuma Sheme Faskari zuwa Garin Gora ta Malumfashi.

Wannan wuri dai yana da matukar mahimmanci a wanna yanzki da kuma sauran al’ummomi da suka saba da zirga-zargar yau da kullun da kuma kasuwanci, sai dai kuma ya yi matukar lalacewar gaske wanda hakan Kan jawo matsalolin hadurra ababen hawa waɗanda suka hada da Motoci da babura wani lokacima harda Masu amfani da kekuna.

Hakan yasa al’umma suke kira ga gwamnantin jihar Katsina karkashin jagora adali gwamna Aminu Bello Masari  da ta ga Allah ta gyara wannan wuri domin ceto mutane daga shiga hadurra da ke lakome rayuka ko jin munanan raunuka.

Da fatan duk wanda yayi ido biyu da wannan roko na al’umma  zai isar da shi gaba domin samun mafita.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *