Ana Zargin Jam’iyyar PDP Ta Maida Wasu Mambobinta ‘Ya ‘Yan Mowa A Katsina
Ana Zargin Jam’iyyar PDP Ta Maida Wasu Mambobinta ‘Ya ‘Yan Mowa A Katsina
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina ta hana wasu daga cikin ‘ya ‘yan ta da ke goyon bayan tsohon sakataren gwamnati Dakta Mustapha Inuwa damar shiga cikin waɗanda za su yi takara a zaɓen jam’iyyar da ke tafe.
Haka dai na zuwa a daidai lokacin da ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP ke neman a ba su damu su sayi fom din takarar shugabancin jam’iyyar a matakin jiha da kuma ƙananan hukumomi tare da mazaɓo a jihar Katsina
Magoya bayan jam’iyyar PDP ɓangaren Dakta Mustapha Inuwa sun ziyarci shalkwatar jam’iyya domin neman a ba su dama su sayi fom din takara, amma ba su iske ‘yan kwamitin riƙon ƙwarya na jam’iyyar PDP ba.
Haka kuma ana zargin cewa shugabannin riƙon ƙwaryar suna biyayya ne kawai ga tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a zaɓen 2023 Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke.
Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan sun ziyarci shalkwatar jam’iyya, ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP, Alhaji Salisu Lawal Uli ya bayyana shakkunsa game da kwamitin rikon kwaryar.
Yana mai cewa kwanaki biyar kafin a rufe sayar da fom din takarar shugabancin jam’iyyar a matakai daban-daban an ga kwamitin rikon kwaryar suna ganawa da wasu ‘yan takarar, amma a yau sun yi ɓatan dabo.
Duk wani yunkuri na ji daga ɓangaren kwamitin rikon kwarya na jihar Katsina ya ci tura a daidai lokacin haɗa wannan rahoto domin jin na su ba a si game da wannan tirka-tirka da taki ci taki cinyewa.
Idan za a yi tunawa tun bayan kammala zaɓen 2023 jam’iyyar PDP a jihar Katsina ta faɗa rikita -rikita wanda har yanzu ba a warware ta ba.
Yanzu dai abin jira a gani shine, ko jam’iyyar PDP zata daidai matsalolin da ke gaban ta, tunda gashi yanzu ana tunkarar zaɓen shuwagabannin jam’iyyar a matakai daban-daban, lokaci shi ne alkali!
