September 18, 2026

An Ƙaddamar Da Kodinetocin Neman Jihar Karaɗuwa Na Kananan Hukumomi 11 A Funtua

IMG-20251019-WA0007

 

Daga Hussaini Yero, Funtua

Shugaban kwamatin fafutukar Neman Jihar Karaduwa daga cikin Jihar Katsina, Alhaji Kabir Aliyu maska ​, ya kaddamar da Kodinetoci shadaya na Kananan Hukumomi shiyar domin fadada ayyukan su na neman Jihar Karaduwa.

Da yake jawabi a lokacin kaddamarwar,Shugaban Babban Kwamitin Zartarwar na fafutukar neman Jihar Alhaji Kabir Aliyu Maska ya bayyana cewa, a yayin taronsu na zartaswar an yanke shawarar a baiwa kodinetoci alhakin tafiyar da al’amuran Kananan Hukumomi ukumominsu, dan samun gudunmuwa ta kowa da kowa dan ganin hakarmu ta cimma ruwa na neman Jihar Karaduwa inji Kabir Aliyu Maska”.

” Ya bayyana cewa duk da wasu matakai da tsare-tsare da suka wajaba idan aka bi su, akwai bukatar masu gudanarwa su wayar da kan al’ummar karkara kan kokarin tabbatar da samun Jihar Karaduwa.

Kabir Aliyu Maska ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu kwamitin zartaswa ya gabatar da takarda ga kwamitocin majalisar Dattawa da na Wakilai kan samar da jihar Karaduwa a Kano da Kaduna a yayin taronsu na amsar bukatun al’umma.

Shugaban ya ce an samu wani gagarumin ci gaba da kuma fatan alheri, domin sama da Sanatoci 72 ne suka amince da kudirin dokar sabuwar Jihar Karaduwa,wanda Sanata shiyar Funtúa Sanata Muntari Dandutse ya gabatar da kudirin a zauren Majalisar”.

” Kabir Aliyu Maska ya ci gaba da cewa yunkurin samar da Jihar Karaduwa ya yi daidai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya”.

“Kuma ya bayyana jindadinsa ga maigirma gwamnan Jihar Katsina Dr Dikko Umar Radda (PhD ) bisa goyon bayan da yake badawa ga yunkurin samar da Jihar karaduwa.

Shima a nasa jawabin, Sakataren Kungiyar Neman Jihar Karaduwa, Eng Tukur Lawal Funtua, ya bukaci Kodinetocin su jajirce wajen ganin an cimma manufofin da ake bukata na samun nasarar samun Jihar Karaduwa.

Yayi Tsokaci akan tarihin yunkurin samar da Jihar karaduwa wanda ya faro shekaru da dama da suka gabata tare da tausayawa kakanninmu .

Eng Tukur Lawal ya ce an tsara wani tsari na ganin cewa harkar ba ta tabuka komai ba a wancan karon.

Sakataren ya kuma yi kira ga kodinetoci da ‘yan yankin na shiyyar Karaduwa da su ci gaba da jajircewa da bin doka da oda da Addu’a Koda yaushe dan samu nasara Jihar Karaduwa.

Anan take Sakataren En, Tukur Lawal ya bayyana Kodinetocin Kananan Hukumomin kamar haka , Hon Sagir Machika daga Karamar Hukumar Sabuwa ,Kankara Hon Mashimu Jobe , Dandume Alhaji Musa Rabiu Mahuta ,Faskari Zubairu Muhammad Sheme, Funtua, Ibrahim Mu’azzam,Musawa Aminu Abdullahi San Inna,Matazu ,Isah Mazoji, Malunfashi Muktar Ammani ,Danja Ibrahim SK,Bakori Hon Habibu Muhammad sai Karamar Hukumar Kafur Dr Bashir Yakubu Kagara.

Kodinetocin ta bakin wakilin su , Ibrahim SK na Karamar Hukumar Danja ,ya bayyana cewa, lallai zasu bazama wajan Fadakar Da al’umma akan wannan gagarimin aiki da aka basu dan samun nasarar Jihar Karaduwa.

Daga cikin Kwamitin Zartarwar na fafutukar neman Jihar Karaduwa da suka halarci taron sun hada ,Halilu Musa Kafur ,Hajiya Aisha Bakori,Iro Musa Anda Funtua da dai sauran su.

About The Author