An Raba Kayan Haihuwa A Karamar Hukumar Mashi Ta Jihar Katsina.
Karamar hukumar Mashi ta ce zata taimakama kokarin gwamnatin jihar Katsina a bangaren kula da lafiya daga tushe.
Shugaban karamar hukumar Salisu Kallah Dankaba ne ya bada wannan tabbacin a lokacin raba kayan haihuwa, kwayoyi da kuma alluran riga-kafi ga mata masu juna biyu da masu shayarwa a yankin.
Ya ce kayan za su taimaka wajen tsallake hadurran da mata masu haihuwa za su iya cin karo da su a yankin.
Ya shawarci matan suyi amfani da kayan yadda ya kamata domin kare lafiyar ƴaƴansu a lokacin haihuwa.
A jawabansu na daban daban, matar kwamishinan kula da ƙananan hukumomin da lamurran masarautu na jihar Katsina Rukkaya Ya’u Umar da kuma Zulaiha Dikko Umar Radda sun ce an raba kayan ne domin kare lafiyar uwa da ɗanta a lokacin haihuwa.
Tunda farko, saida jami’in kula da lafiya daga matakin farko na karamar hukumar Kabir Shehu Kaita ya yi kira ga mata masu juna biyu suyi amfani da kayan haihuwar domin kare lafiyar abinda suka samu.
Ya kuma ce ko tantama babu kayan zasu taimaka wajen yin tsaftar jiki a lokacin da aka sauka.
