An Bukaci Yan Siyasar Da Suka Aje Mukamai Su Bayyana Kadarorinsu A Katsina.
Ofishin hukumar kula da da’ar ma’aikata na Jihar Katsina ya yi kira ga kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman da suka yi murabus bisa radin kansu da su zo ofishin su karbi fom din bayyana kadarorinsu.
Hakan dai na cikin tanadin sashen na 3 da 5 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Ofishin ya bayyana cewa, tanadin na kundin tsarin mulkin Najeriyar ya yi bayanin cewa, dukkan wanda zai amshi wani mukami sai ya bayyana kadarorinshi kafin shiga ofishi da kuma bayan ya bar ofishin.
Kamar yadda hukumar ta bayyana, kin bayyana kadarorin ya saba ma dokokin kundin tsarin mulkin Najeriya da suka kafa hukumar kula da da’ar ma’aikatan.
Kuma bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktar hukumar Halima Sabi’u Mahuta ta sanya ma hannu.
