September 18, 2026

An Bukaci Maniyyata Aikin Haji Su Nemi Ilimin Addinin Muslumci A Shiyyar Funtua.

0

Daga Auwal Isah

An bukaci masu niyar zuwa aikin hajin bana a shiyyar Funtua su nemi ilimin addinin Muslumcin don sanin yadda za suyi aikin haji kafin su bar gida Najeriya.

Jami’in kula da aikin haji na jiha a shiyyar Alhaji Isah ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinshi.

Ya yi kira ga maniyyatan da su rika zuwa taron kara ma juna sani da ake yi akan aikin haji a kananan hukumomi 11 na shiyyar.

Kamar yadda ya bayyana, manufar hakan ita ce don su sabunta iliminsu akan tsare tsaren aikin hajin.

Alhaji Isah ya yi nuna da cewa, akwai maniyyata aikin haji a bana daga shiyyar sama da 689, kuma wasu ma na zuwa.

A wani labarin kuma, jami’in aikin hajin na shiyyar Funtuar ya ce maniyyata aikin hajin banar za su je a tantance lafiyarsu a ranar wannan Litinin din da ke tafe.

Kamar yadda ya ce, aikin tantance lafiyar shi ne zai ba hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Katsina damar samun bayanan da take so da za a san matsayin maniyyatan.

Ya kara da cewa, za a yi ma maniyyatan rigakafi a nan gaba kuma.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *