September 18, 2026

An Bukaci Gwamnatin Katsina Ta Gyara Hanyar Ketare-Gidan Maijimina.

0

Wani dan kishin kasa mai suna Adamu Mai Waya Gidan Kerau ya yaba ma gwamnatin jihar Katsina bisa gyaran hanyar Kankara zuwa Katsina da ke gudana yanzu haka.

Dan kishin kasar ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya ziyarci dakinmu na labarai.

Kamar yadda ya bayyana, idan aka kammala gyaran hanyar za ta bunkasa tattalin arzukin al’umma.

Adamu Mai Waya ya kuma yi kira da a gyara hanyar Ketare zuwa Gidan Maijimina.

Shima Bello Mai Kama Sani Ba Igiya da ya bada gudunmuwarshi a lokacin ziyarar, ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta gyara makarantar firamarin Chakau da ke cikin karamar hukumar Danmusa duba da yadda take cikin mawuyacin halin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *