An Bai Yan Kasuwar Kwanar Gafan Wa’adin Kwana Bakwai Su tashi da wajen da suke Sana’a
Daga Dantala Uba Nuhu Kura, Kano
Majalisar karamar hukumar Garun mallam a jihar Kano, ta ba mazauna kasuwar Kwanar Gafan wa’adin kwana bakwai da su tashi daga cikinta har zuwa wani lokaci nan gaba.
Shugaban karamar hukumar, Hon Barr Aminu Salisu Kadawa ne ya bada umarnin hakan a wajen bikin kaddamar da sake fasalin farfado da tattalin arzikin yankin.
Kadawa ya ce “Duba da irin yadda kasuwar aka mai da ita tamkar wata mafaka da cibiyar yada badala maimakon ainihin abun da aka kafa kasuwar tun farko da shi.
Sai ga shi an buge da yin abubuwan da suka sha banban da manufar kasuwar. Don haka ya bukaci mazauna kasuwar da su tattara kayansu su bar wajen, tun kafin ranar 1 ga watan Janairu 2025.
Ya ce “Duk wanda aka kama za a hukunta shi. Inda ya bayyan cewar nan gaba za a bayyana lokacin da za a yi bikin sake bude ta don cigaba da kasuwanci iri daban-daban ba ma na kayan Gona ba har nau’in sauran ababan more rayuwa.
Daga karshe ya bukaci yan kasuwa da su zo don saka jarinsu a kasuwar. Wani malamin addinin islama, Imam Abdullahi Yusif Chiromawa, ya yi jawabi akan yadda kasuwar Kwanar Gafan ke barazana ga tarbiyar yaransu, ya ce abun ba dadin ji balle gani.
Malam Abdullah ya ce “Kasuwar ta zama wajen aikata zinace-zinace ,Luwadi, da yin madigo ga matasa da kuma kawo matan aure kasuwar da daddare.
Daga nan ya kara da bayyana kasuwar a matsayin wata mafakar Barayi da yan fashi da masu safarar mungan kwayoyi.
Imam Abdullahi, ya gode wa shugaban karamar hukumar bisa namijin kokarin da yanuna don kaucewa kara fadawa cikin fushi Allah
Tun da fari a nasa jawabin, kwamishinan yan sandan Kano, S.A Gusau kuma babban bako a wajen, ya ce “tuni tunaninsu ya ke kan kasuwar Gafan yadda za su kawo karshen mazauna cikinta bayan karewar kayan noman rani.
Amma lokaci ya yi da hukumar tsaro za ta sa’ido ta ga masu tsauri-Ido. Kuma nan take ya bada umarni daga ranar 25 ga watan Disamba 2024 kowa ya bar kasuwar.
A karshe taron sabunta kasuwar kwanar Gafan ya samu halartar manyan baki .
