November 18, 2026

Abubuwan Da Za Su Iya Faruwa Da APC Idan Akayi Gangancin Tsayar Da ƊangiwaTakarar Gwamna

0

Daga Gaddafi Kusada

Wannan Hasashe nane zai iya kasancewa Gaskiya Ko Aƙasin Hakan.

‘Yan Katsina mazauna Abuja zaɓabu tuntuni suka ja layi babu wani hasashe ko da a mafarki da zai iya muni da cewa zasu marawa takarar DANGIWA baya In banda Abubakar Yahaya Kusada shi ɗaya ne tun daga kan Sanatoci da ‘yan majalisun tarayya

Idan muka dawo gida kuma ɓangaren Dakta Mustapha Inuwa shima Ina da tabbacin a kwarewar siyasa irin tashi ba zai yarda a bautar da tunaninsa dana jama’arsa da sunan marawa Ɗangiwa baya ba

Waken suya mataimakin gwamna Mannir Yakubu bana tunanin koda a mafarki wannan bawan Allah zai janye makaman yakinsa domin ya marawa Dangiwa baya ba….

Umar Abdullahi Tata koda wasa bana Iya jin Tata zai sahale ya marawa Dangiwa baya ba….

Sanata Hadi Sirika duk da har yanzu babu wata shaida ta zahiri ko ta badili da ta nuna Sanata Hadi yana neman kujarar gwamna bani shayi ko shakkar ko da ba zai neman ba zai marawa Dangiwa baya…

Mu bulla wajan Dakta Dikko Umar Radda Gwagware shi ka dai ne nake da tabbacin zai marawa Dangiwa baya ko yana so ko baya so Idan MASARI ya umarce shi saboda wata magana da na ji ya yi a kwanakin baya

A takaicen takaicewa dai a karshen yaran ƊANGIWA za’a bari daga shi sai halinsa a filin zaɓe

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *