September 18, 2026

Ƙwamitin Tantance ‘Yan Takarar Shugabancin Jam’iyyar APC Na Kasa Ya Kammala Aikinsa

0

Daga SSA AbdulHadi Ahmad Bawa

Kwamitin da jam’iyyar APC ta ɗora ma alhakin tantance masu neman tsayawa takarar muƙaman shuwagabannin jam’iyyar na kasa, karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, yana ci gaba da aikin shi kamar yadda aka tsara.

Wannan Kwamitin yana cike da manyan ɗiyan jam’iyyar wanda suka haɗa da tsohon kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya Hon. Oladimeji Bankole, tsohon Gwamnan Jihar Borno Alhaji Maina Ma’aji Lawan, Werinipre D. Seibarigu.

Sauran sun haɗa da Sanata Aishatu Dahiru Binani, Sanata Ibrahim Hassan Hadeja, Alhaji Abdullahi T. Gwarzo da sauran su, sai kuma Sakataren kwamitin Barista Emmanuel Chukwuemeka.

Ya zuwa yanzu, kwamitin ya gama tantance masu neman tsayawa takarar Shugaban Jam’iyya, Muƙaddashin shi, Mataimakan shi na shiyyoyi da kuma Magatakardan jam’iyyar. Ana kuma ci gaba da tantance sauran masu neman tsayawa takarar.

Addu’ar mu Allah Yasa a gama lafiya, Shi mana zaɓi mafi alkhairi kuma Ya tsare mana jihar mu da ƙasar mu baki ɗaya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *