A Shiyyar Funtua: Wa Ya Kamata Ya Yi Wa Dikko Raɗɗa Mataimaki?
Daga Dakta Bashir Abu Sabe
Tuni dai jam’iyyun siyasa wadanda suka tsayar da ‘yan takarkarin gwamna suka fitar da waɗanda za su yi masu mataimaka.
Jam’iyyu biyu masu ƙarfi a jihar Katsina, sun fitar da mataimakan da suka ƙara wa tafiyar jam’iyyar tasu armashi.
PDP ta fitar da Ahmad Aminu, wani gogaggen ma’aikacin gwamnati, kuma ɗan siyasa.
NNPP ta fitar da Dakta Muttaƙa Rabe Darma, ɗan siyasa, malamin makaranta, kuma masanin aikin gwamnati.
Waɗannan mataimaka guda biyu, tamkar sun yi hannunka mai sanda ne jamiyyun suka yi wa jam’iyyar APC, cewa dole ta yi tunani da hangen nesa a kan wa za su ɗauko.
A tsarin jam’iyyar na daidaito ba za ta iya ɗauko mataimaki daga shiyyar Daura ba.
Dalili, shugaban jam’iyya APC daga can yake. Mai ba jam’iyyar ta ƙasa shawara a kan harkokin shari’a daga can yake. Shugaban ƙasa daga can yake. Minista daga can yake. Akwai manyan kujerun gwamnatin jiha da Tarayya, duk daga can suke.
Hatta karfin yawan kuri’u da masu jefa kuri’a, yankin Funtua ya fi Daura.
PDP da NNPP sun fitar da ɗan takarar gwamnoninsu daga yankin na Funtua. APC na son tabbatar wa da yankin suna tare, shi ne su ba su mataimakin gwamna.
A yankin Funtua, mutane da yawa suna da sha’awa, amma mutane huɗu ne sunansu ya yi tambari.
Daya daga cikin su, dokar ƙasa da ta hukumar zaɓe sun haramta masa duk wata takara, domin bai da takardar makarantar da dokar ƙasa ta amince ya yi takarar.
Uku duk sun cancanta. Na farko, Dakta Aminu Garba Waziri, babban sakataren ma’aikatar gona ta jihar Katsina. Ya taɓa riƙe shugaban karamar hukumar Malumfashi. Kuma ya kafa tarihi mai kyau.
Malamin makaranta ne, ɗan siyasa, kuma masanin aikin gwamnati.
Na biyu Musa Adamu Funtua. Tsohon kwamishinan ƙananan hukumomi a jihar Katsina yanzu kwamishinan Ruwa na jihar, jajircaccen dan siyasa ne, saboda alherin shi ana masa kirari da Glo babban layi. matsalar sa ya fito daga cikin garin Funtua, wanda suna da ɗan takarar sanata.kuma ɗan uwa ne na jini shaƙiƙi da wanda samu tikitin Sanata a jam’iyyar APC.
Na uku, Hamza Sule Faskari. Kwamishinan Muhalli na Jihar Katsina. Dalilai da yawa suka sanya, Hamza Sule ya yi zarra a takarar.
Na farko, shi mutum ne mai biyayya da riƙe amana. A tsawon zaman kujerarsa, ya riƙe amanar gwamna Aminu Bello Masari a siyasace.
Ƙananan Hukumomi biyu Faskari da Sabuwa da ke ƙarƙashin kulawarsa a siyasance ba su taɓa kaucewa ba.
Ko a zaɓen fitar da ɗan takarar da aka yi na gwamna, bisa umurnin da ya samu daga gwamna, kuri’un Faskari da Sabuwa baki ɗayansu Dakta Mustafa Inuwa suka jefa wa.
Na biyu, yana tare da siyasar gidan Dakta Mustapha Inuwa, ba shi mukamin zai faranta wa bangarensa rai, kuma za su rage zafin raɗaɗin da suke ji.
Na uku, ya fito daga gidan siyasar Abu Ibrahim, wanda sun taka rawa sosai wajen ganin Dikko Raɗɗa ya yi nasara a zaɓen fitar da ɗan takara.
Na huɗu, Kwamishinan Muhalli da yake riƙe da shi a jihar Katsina ya sanya sunansa ya shiga ko’ina sakamakon ayyukan da ma’aikatar ta yi, wanda ya karaɗe Jihar, kuma ana ganin amfaninsu, musamman yanzu lokacin damina.
Na biyar, Hamza mutum ne mai alheri, wanda sunansa ya karaɗe jihar. Don haka ba zai wahalar sai da wa ba.
Na shida, duk yankin Funtua, Hamza ba shi da abokin faɗa ko husuma ta siyasa, kowa nasa ne, dattawa, matasa da matsakaita.
Na bakwai, Hamza yana da kuɗin kansa, ba wanda zai jira sai an ba shi ba ne, idan aka ba shi takarar zai nemo kuɗin da za a taimaka wa takarar da su.
Na takwas, Hamza yana cikin rukunin matasa mai kwazo da kumaji. Tarihinsa cike yake da neman na kai tun kafin shigar sa ya siyasa.
Na tara, yana da ilmi a karance da aikace na tafiyar da jama’a, mulki da kasuwanci.
Idan jam’iyyar APC tana son daidaita sahun gumurzun da za ta shiga a zaɓen 2023, zaɓen Hamza Sule Faskari a matsayin mai mara wa Dikko Raɗɗa baya, shi ne daidai da ita, kuma daidai da hali da yanayin da ake ciki da wanda za a shiga
