September 16, 2026

A cigaba da ziyarar wayar da kai da

0


Dr Lawal Usman Bagiwa yake akan shirin noman ciyawa da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin jihar Katsina ta samu tallafin kudi naira biliyan shidda da miliyan dari biyu daga gwamnatin tarayya domin yinkurin magance matsalar tsaro musamman a kananan hukumomi guda goma na jihar da matsalar ta shafa.
A yau cikin ikon Allah Dr. Bagiwa mai ba mai girma Gwamnan jihar Katsina shawara akan kiwon dabbobi da gandun daji tare da yan kwamitin shirin sun fara isa fadar mai girma yan dakan Katsina hakimin gundumar Dutsinma inda Dr Bagiwa ya bayyana mashi manufar shirin da irin gudunmuwar da zasu bada acikin shirin domin samun nasara, a take yan dakan Katsina yayi naam da shirin tare da bada tabbacin zasu bada goyon baya dari bisa dari ,kana yace a mika masu sakon godiyar su ga mai girma shugaban Kasa da mai girma Gwmnan jihar Katsina Rt.Hon Aminu Bello Masari abisa wannan muhimmin aiki da zaayi masu, kana yace tabbas yin wadannan ayyuka zai rage matsalar tsaro da ake fuskanta a jihar Katsina.
Daga nan Dr Lawal Usman Bagiwa ya jagoranci tawagar zuwa garin Safana da Danmusa domin cigaba da wayarma al’ummar garin da kai ,inda suma ya zayyano masu muhimman ayyukan da zaa yi masu kamar haka:
Gina gonar ciyawa
Gina asibiti ta mutane domin makiyaya
Gina abisitin dabbobi domin kula da lafiyar dabbobin makiyayan
Gina hanyoyi
Gina burtali da gyara wadanda ke ake dasu
Gina makarantar boko ta (Nomadic primary school) tare da gyaran wadanda ke da kwai
Gina Dam da gyara wandanda ake dasu
Gina mayanka
Gina wajen hutawa na makiyaya
Da kuma bada tallafi na abinda mutane suka zaba da kansu.
Dr. Bagiwa yace wadannan sune muhimman ayyuka da muka zo muyi maku albishir gwamnatin jihar Katsina ta shirya domin tazo tayi maku su, abisa haka ne zamu baku sati guda domin ku hadu da sauran masu ruwa da tsaki na garuruwanku domin ku shawarta ku kawo mamu rahoto inda kuka zaba kuke so ayi maku ayyukan nan tare da tallafin da kuka zaba ayi ma mutanen ku, muna fatan zaku ba gwamnati hadin kai domin a aiwatar maku da ayyukan.
Shugaban karamar hukumar Safana dana dan Musa sun yi marhabun lale da wadannan ayyuka tare da jadda aniyarsu ta bada goyon bayan su dari bisa dari domin karba wannan shiri da hannu biyu biyu.
Haka kuma masu girma Hakimman Safana da zakka Alh Sada Rufa’i Yariman Safana Hakimin Safana da Alh Sani Zakka Hakimin zakka suma sun bada nasu tabbacin goyon baya tare da godiya ta musamman ga mai girma Gwamnan jihar Katsina.
Dr. Bagiwa ya samu rakiyar wasu kamar haka: Hon Abubakar Tunas dan majakisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Ingawa kuma shugaban Kwamitin lura da harkokin ma’aikatar gona ta jihar Katsina, Alh Mannir Atiku, Chairman Miyatti Allah na jihar Katsina, Alh Sani Danjari Wakilin shugaban kungiyar manoma ta jihar Katsina, Hon Abdulkarim Ibrahim S.A security wakilin mai ba mai girma gwamnan jihar Katsina shawara a fannin tsaro, Daraktocin ofis da sauran ma’aikatanshi na ofis.
Rahoto Daga ofis din Darakta Janar Soshiyal Mediya na mai girma Gwamna .

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *