KANNYWOOD: Ko Dai A Gyara Ko Ta Wargaje!
Daga: ALIYU A. GORA II
Lallai Bahaushe ya yi gaskiya da ya ce daga kin gaskiya sai bata. Har na tuna lokacin da muke kokarin gyara wa ‘yan fim zama a Mujallar Fim, amma a wancan lokacin hatta ‘yan kallo cewa su ke wai hassadar su mu ke yi.
Kuma har yau din nan, akwai ‘yan Fim da dama masu kallon mu a matsayin makiyan su, kuma kawai saboda mun ce a gyara can a daidaita can.
Yau ga shi an wayi gari da kan su sun fara fallasa kazantar da ke faruwa a Kannywood.
Sakacin manyan Kannywood ya janyo sannu a hankali kananan yara su ka fi karfin su.
Manyan jarumai da daraktoci sun sha bada kudi don a kai mu kotu, kawai don mun wallafa labarin da wani ke ganin kamar cin zarafin shi aka yi.
A wancan lokacin, duk yarinyar da ta kauce hanya, da mun yi mata hannun ka mai sanda a Mujalla sai ogan ta ya dauki waya, ya kira mu ya yi ta zunduma mana zagi.
Ba komai, amma ina mai ba ‘yan fim shawara, daukar bidiyo su na wallafawa a dandalin sada zumunta, tamkar su na gaskata zarge-zargen da su ke yi wa juna ne.
Kuma abin kunya, saboda rashin kyakkyawan tsari, manyan Kannywood an rasa wanda zai tsawata, a kuma tilasta kowa ya goge bidiyon da ya wallafa.
Da ma duk wanda ya kauce wa tsarin Allah, to tabbas ba zai ga daidai ba.
Kiri-kiri, an san mutum ba daidai ya ke yi ba, amma duk wanda ya tsawata don a gyara, to daga rannan shi makiyi ne kuma mai hassada.
Gaskiya dai daya ce, daga kin ta kuma sai bata.
Ya na da kyau manyan Kannywood su taka wa yaran su birki a kan fallasar da su ke yi wa juna a Social Media Pls 🙏
