November 19, 2026

Gwamna Jihar Zamfara Ya Ƙaddamar Da Aikin Hanyoyi Da Za Su Haɗa Ƙananan Hukumomi Huɗu

IMG-20261106-WA0010

 

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada aniyar gwamnatin sa na inganta rayuwar al’umma ta hanyar samar da muhimman ababen more rayuwa, yana mai cewa gina manyan hanyoyin da za su haɗa ƙananan hukumomi huɗu na jihar na daga cikin matakan da gwamnatin sa ke ɗauka wajen cimma wannan buri.

 

A ranar Talata ne gwamnan ya ƙaddamar da aikin gina hanyoyin Tashar Abu zuwa Kekun Waje zuwa Bingi, da ke Ƙaramar Hukumar Bungudu; hanyar Kwatarkwashi zuwa Mada; da kuma hanyar Gusau zuwa Jauri, Dogon Kade, Dan Isah, Nasarawa Mai Layi da Nasarawa Godel. Waɗannan hanyoyi za su haɗa ƙananan hukumomin Gusau, Bungudu, Kauran Namoda da Birnin Magaji.

 

A cewar sanarwar da Mai Magana da Yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, aikin Tashar Abu, Kekun Waje zuwa Bingi zai ƙunshi sake gina hanyar, aikin shimfiɗa ƙasa, gina shimfiɗar kwalta a matakai biyu, magudanan ruwa da kuma matakan daƙile zaizayar ƙasa. Ana sa ran kammala aikin cikin watanni 18.

 

Sanarwar ta kuma bayyana cewa an bai wa kamfanin Zhongcheng Construction Nigeria Limited kwangilar sake gina hanyar Kwatarkwashi zuwa Mada, inda aka tsara kammala aikin cikin watanni 12.

 

Haka kuma, an bai wa kamfanin CCECC Nigeria Limited kwangilar gina hanyar Gusau zuwa Jauri, Dogon Kade, Nasarawa Mai Layi da Nasarawa Godel, wadda tsawonta ya kai kusan kilomita 53. Ana sa ran kammala wannan aiki cikin watanni 18.

 

Yayin ƙaddamar da matakin ƙarshe na aikin hanyar Gusau zuwa Nasarawa Godel, Gwamna Lawal ya bayyana waɗannan ayyuka uku a matsayin muhimman nasarori a shirin gwamnatinsa na “Aikin Ceto”, wanda aka ƙaddamar da shi domin farfaɗo da kyakkyawan fata a zukatan al’umma, sake gina ababen more rayuwa, inganta tsaro da faɗaɗa hanyoyin samun ci gaba ga al’ummar jihar.

 

Gwamnan ya ce, “Gwamnatinmu ta fahimci cewa ingantattun hanyoyi na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziki, inganta tsaro, ci gaban zamantakewa da kuma kyautata rayuwar al’ummarmu baki ɗaya.

 

Wannan ne ya sa muke ci gaba da ba da fifiko ga ayyukan da za su inganta rayuwar ’yan ƙasa kai tsaye, tare da ƙarfafa alaƙar sufuri tsakanin sassan jihar.

 

“Wannan aikin zai shafi ƙananan hukumomi huɗu kai tsaye, inda aka tsara rabon tsawon hanyar kamar haka: kilomita biyar a Ƙaramar Hukumar Gusau, kilomita 12 a Ƙaramar Hukumar Bungudu, kilomita tara a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda da kuma kilomita 27 a Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji.

 

“Ayyukan da za a gudanar ba su tsaya ga shimfiɗa ƙasa kawai ba, sun haɗa da gina magudanan ruwa masu girma da nau’o’i daban-daban, magudanan ruwa na ƙarfafan siminti a wuraren da aka gano akwai buƙata, matakan daƙile zaizayar ƙasa da kare wuraren da hakan ka iya shafa, da sauran ayyukan da suka dace domin tabbatar da inganci da dorewar hanyar.

 

“Haka kuma, aikin ya ƙunshi gina gadoji guda uku, waɗanda za su kasance da tsarin sassa uku, sassa biyu da kuma sassa goma, domin sauƙaƙa zirga-zirga da tabbatar da tsallakawa cikin aminci da kwanciyar hankali a dukkan sassan hanyar.”

 

Gwamna Lawal ya jaddada cewa kammala waɗannan ayyukan hanyoyi zai haɗa al’ummomin yankunan da hedikwatocin ƙananan hukumominsu, da kuma Gusau, babban birnin jihar.

 

Ya ce hakan zai sauƙaƙa zirga-zirga da jigilar kayayyaki, rage kuɗin sufuri da lokacin da ake ɗauka wajen tafiya, tare da inganta damar samun kasuwanni da muhimman hidimomin yau da kullum. Haka kuma, zai taimaka wa manoma wajen kai amfanin gonakinsu kasuwa cikin sauƙi.

About The Author