DG Kamfen Na Shugaban Kasa Sanata Yari Ya Gudanar Da Taron Masu Ruwa Da Tsaki Na APC A Zamfara
Daga Hussaini Yero,Gusau
Darakta Janar na Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Shugaba Bola Ahmad Tinubu na zaɓen 2027, Sanata AA Yari ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a wani taro a gidansa na ƙauye da ke Karamar Hukumar Talata Mafara.
Da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan taron, Sanata AA Yari ya ce ya yanke shawarar gana da masu ruwa da tsaki domin Neman cikakken goyon baya ga Shugaban Ƙasa a Zabeshi a 2027.
Ya tabbatar da cewa Jihar Zamfara za ta kada wa Shugaba Bola Ahmad Tinubu ƙuri’a mai yawa a lokacin zaɓe.
Ya ƙara da bayyana cewa dole ne ya fara aikinsa daga gida, domin yana sa ran samun cikakken goyon baya da ƙuri’u daga Zamfara, wadda jihar APC ce kuma shi ɗan Jihar ne. Haka kuma mutanen Zamfara suna yabawa Shugaban Ƙasa bisa shi wannan babban alhaki na DG PCC.
Ya ce masu ruwa da tsaki sun ba da tabbacin cikakken goyon baya, haɗin kai da ƙuri’u wajen tallafawa Shugaban Ƙasa ya sake dawowa mulki a 2027 na wa’adi na biyu.
Yari ya ce Shugaban Ƙasa yana yin iya ƙoƙarinsa wajen magance matsalar rashin tsaro, musamman a Zamfara da sauran sassan ƙasar.
Ya ce PCC za ta yi yaƙin neman zaɓe ne bisa nasarorin da Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya cimma waɗanda kowa ke iya gani.
Ya yi kira ga dukan magoya bayan APC da ‘yan Najeriya da su tallafawa burin Shugaba Bola Ahmad Tinubu na komawa Bila a zaɓen 2027.
Manyan mutane a jam’iyyar APC na Jihar Zamfara ne suka halarci taron.
