APC ta tabbatar da Dikko Raɗɗa a matsayin ɗan takarar gwamna karo na biyu a Katsina.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya samu amincewar jam’iyyar APC a matsayin ɗan takarar gwamna domin fafatawa babban zaɓen shekarar 2027.
An tabbatar da shi ne a yau alhamis a filin ‘People’s Square’ da ke gidan gwamnatin Katsina, bayan wani tsarin maslaha da ya haɗa wakilan jam’iyyar daga sassa daban-daban na jihar Katsina
Adadin jimlar wakilai da suka halarci taron sun kai 2,872 da suka tabbatar da wannan takara, ciki har da wakilan ƙananan hukumomi, na jiha, da kuma na mazaɓo.
Shugaban kwamitin tabbatarwar APC, Dr. Yakubu Ahmed Maccido, ya bayyana cewa an gudanar da tsarin cikin gaskiya tare da bin ƙa’idojin jam’iyyar APC.
Ya ce an gudanar da amincewar ta hanyar ƙuri’ar baki, wadda ta nuna cikakken goyon baya ga gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa.
“A sakamakon haka, muna ayyana Malam Dikko Umaru Raɗɗa a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamnan APC a Jihar Katsina domin zaɓen shekarar 2027,” in ji Maccido.
A nasa jawabin, tsohon gwamna Aminu Bello Masari ya gode wa Allah bisa nasarar gudanar da tsarin cikin lumana, yana mai bayyana cewa tsarin ya gudana cikin gaskiya da riƙon amana.
Masari ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyyar APC da su ci gaba da mara wa gwamnatin Gwamna Raɗɗa baya tare da goyon bayan shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A jawabin sa na karɓar tikitin takarar gwamnan, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya gode wa mambobin jam’iyyar bisa amincewar da suka sake nuna masa a karo na biyu.
Ya ce zai ci gaba da mayar da hankali wajen samar da kyakkyawar shugabanci, ayyukan ci gaba da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar Katsina
