Yan Sanda Sun Damke Wanda Ake Zargi Da Kitsa Kai Hare-haren Da Garkuwa Da Mutane a Katsina
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta yi nasarar cika hannu da wani mai suna surajo Isiyaku da ake zargi da hannu akan garkuwa da mutane da satar shanu da kuma baiwa barayin daji bayanan sirri a Katsina.
Kakakin rundunar a Katsina DSP Sadiq Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka a wata sanarwar da ya fita ga manema labarai a Katsina.
Sanarwar ta ce mutumin ɗan kimanin shekaru 45 a duniya ya addabi yankin Matazu da kewaye wajen jagorantar kai hare-haren wuce gona da iri musamman garin Sayaya.
Haka kuma sanarwar ta cigaba da bayanin cewa a ranar 15 ga wannan watan ne jami’an tsaron ‘yan sanda suka samu sahihan bayanai da suka kai ga nasarar damke wanda ake zargi da wannan ɗanyen aiki.
“Ya yin gudumar da bincike wanda ake zargin ya amsa laifuffukan da ake tuhumar da da su, inda ya yi ƙarin haske da cewa wani mai suna Babaye wanda hukuma ke nema kaura wanbai ya haɗa da gawurtaccen ɗan bindiga mai suna Bello” inji sanarwar
Sanarwar ta ƙarar da cewa wanda ake zargi ya faɗa da baƙin sa cewa, sau biyu ana haɗa baki da shi wajen yin garkuwa da mutane a kauyen Sayaya inda aka karɓi kuɗin fansa Naira miliyan 7 kuma an bashi N900,000 a matsayin na shi kason.
Kazalika an zargi Surajo isiyaku da hannu wajen gayyato ƙasurgumim ɗan bindiga Bello inda aka sace shanu 14 a kauyen Dukawa sannan aka ba shi N40,000 lada, kuma yana da hannu wajen kai hare-hare da suka yi sanadiyar kune gidaje da motoci
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina CP Ali Umar Fagge ya ce ana cigaba da ƙoƙarin ganin ta cika hannu da sauran waɗanda ake zargin domin su fuskanci kuliya manta sabo da zaran an kammala bincike
