Marigayi Janar Sani Abacha Abokina Tun Muna Sikandire –Abdulsalam Abubakar
Daga Wakilinmu
Tsohon shugaban Nigeria na mulkin soja ya ce saura kaɗan ayi mashi ritayar dole a lokacin da ya ke aikin soja.
General Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya sanar da hakan ne a lokacin zantawa da shi a gidan talebijin na Trust Television a Abuja.
Kamar yadda bayyana, duk da dangantakar da ke tsakanin shi da tsohon shugaban Nigeriar marigayi Sani Abacha, amma wasu ‘ƴan tawagar shi saida su ka yi ƙoƙarin yi mashi ritayar dole daga aiki.
Saidai ya ce Allah ya ba shi ikon tsallake yunƙurin.
Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya ce shi da Janar Sani Abacha abokai ne tun lokacin da suna makarantar Sikandire.
Kuma ya bayyana tsohon shugaban ƙasar a matsayin mutum mai gaskiya da riƙon amana ga abokan shi.
