September 19, 2026

Hadin Kai Na Da Mahimmaci A Tsakanin Musulmi – Fitiyanul Islam

0

Daga Awwal Isah, Katsina

Shugaban ƙungiyar Manazzamatul Fitiyanul Islam ya bayyana mahimmancin haɗin kai a tsakanin al’ummar Musulmi.

Sheikh Isaq Nuhu Batagarawa ya bayyana hakan ne a lokacin ƙaddamar da wani sabon masallacin Juma’a a ɓangaren Ƴan Gwari cikin kasuwar Ƴarkutungu a nan jahar Katsina.

Shugaban ƙungiyar wanda ya yi jawabi ta bakin sakataren ƙungiyar, Sheikh Ibrahim Idris Gora ya buƙaci mutane da su kula da masallacin yadda ya kamata.

Ya kuma yaba ma wanda suka bada gudunmuwa wurin kammala ginin masallacin.A tsokacin shi lokacin buɗe masallacin, Sheik Labaran Imam Saulawa ya yi kira ga al’ummar yankin da su ci gaba da yin sallolin su a ciki.

Ya kuma buƙaci al’ummar Musulmi da su nemi ilimin addinin Musulumci, wanda shi ne matakin farko na bauta ma Allah.

A saƙon shi na godiya, shugaban kasuwar Ƴarkutungun Alhaji Muhammad ya bada tabbacin taimaka ma kwamitin masallacin don ganin an kula da shi yadda ya kamata.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *