September 18, 2026

Za a yi Taron Tantance Jaruman Fim Ɗin “Kwaryar Sama” Gobe Alhamis A Kano 

IMG-20250709-WA0026

 

Za a yi Taron Tantance Jaruman Fim Ɗin “Kwaryar Sama” Gobe Alhamis A Kano
DAGA MUKHTAR YAKUBU
Idan Allah ya kaimu gobe Alhamis 10 ga Yuli za a yi taron tantance Jaruman da za fito a sabon ɗin “Kwaryar Sama” Wanda  za a fara ɗauka nan da ‘yan kwanaki kaɗan masu zuwa.
Fim din wanda fitaccen furodusa Zaharadeen Jalabi  ya ɗauki nauyin shiryawa  kuma furodusa Usman Ahmad Usee zai kasance mai kula da shirin.
Sai kuma Yunusa Mu’azu  da Nura Mai Shabbabu Mubarak za su kasance masu bayar da umarni.
Haka kuma marubuci Aminu Idris Abdullahi ya jure basirarsa wajen rubuta labarin fim ɗin
Taron tantancewar na maza da mata  zai kasance a tun daga misalin karfe 10 na safe har zuwa yamma a harabar gidan Talabijin na Abubakar Rimi ARTV da ke titin Maiduguri a Unguwar Hotoro da ke cikin garin Kano.
Kazalika ana sa ran zai samu halartar manyan baki kamar shugaban hukumar tace finafinai ta Jihar Kano Abba El-Mustapha da shugaban kungiyar Arewa Film Makers tare da kungiyar Jarumai da na MOPPAN.
Don haka furodusa Zaharadeen Jalabi yake gayyatar dukkan masu sha’awar shiga cikin fim ɗin ko kallon yadda tantancewar zata kasance da su halarci wajen taron da misali karfe 10 na safiyar ranar Alhamis ɗin domin shiga cikin tantancewar ko kallon yadda za ta kasance.

About The Author