Wata Kungiya Nasan Sanata Yar’adua Ya Tsaya Takarar Gwamnan Jihar Katsina A 2023 Domin Ceton Al’umma
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Wata kungiyar Siyasa mai ragin samar da shugabanci na gari (Alliance for Democracy and Purposeful Leadership) na kira da babar murya ga tsohon Sanatan Katsina ta tsakiya, Sanata Sadiq Yar’adua da ya fito takarar gwamna jihar Katsina domin ceton jihar Katsina daga matsalaolin tsaro, tattali arziki da rashin aikin yi da ya addabe ta
Kungiyar ta ce tsohon Sanatan Katsina ta tsakiya shi ne mutun mafi cancanta ya gaji gwamna Aminu Bello Masari a shekara 2023 wanda suke rokonsa da ya amsa wannan kira da ya tsaya takarar gwamnan jihar Katsina a kakar zabe mai zuwa.
Wannan kira ya fito ne daga bakin Shugaban kungiyar, Kwamared AbubakarHamza a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a Katsina, inda ya ce duk da kokarin da gwamnatoci suke yi a matakin tarayya da jiha amma Katsina ta koma wani sansanin mutuwa da lalacewar dukiyoyin al’umma.
“A irin wannan yanayi ne muke bukatar mutun mai nagarta wanda zai jagoranci tafiyar da wannan jiha a siyasa wanda yanzu haka take neman sake kafa wani sabon tarihi wanda zai amfani mutanen jihar da Kasa baki daya” inji shi
Kusan kananan hukumomi goma da ke iyaka da jihar Kaduna da Zamfara suke fuskanta harin wuce gona da iri daga ‘yan bindiga wanda hakan ya haifar da tsoro da rashin tabbas a tsakanin al’umma inda yanzu jihar ta zama fili ko sansani mutuwa da asarar dukiyiyo
A cewarsa a irin wannan hali na rashin tabbas da ake fama da shi na tsaro da tabarbarewar tattalin arziki da jihar Katsina ke fuskanata, Sanata Sadiq Yar’adua ne kadai zai iya fidda jihar daga wannan barazana da take ciki
Kamar yadda Kwamared ya bayyana, idan har aka samu amincewar Sanata Sadiq Yar’adua ya amsa kira da ake yi masa na ya i tsaya takara kuma aka samu nasara, babu shakka matsalar tsaro da rashin aikin zai rago ainun tare da farfado da tattali arziki a jihar Katsina baki daya
