September 18, 2026

Taron  Ƙaddamar da littafin SIRRIN MACE MUSULMA ya kara Farfaɗo da harkar adabin Hausa

IMG-20250524-WA0001

Taron  Ƙaddamar da littafin SIRRIN MACE MUSULMA ya kara Farfaɗo da harkar adabin Hausa

Daga Mukhtar Yakubu
A daidai lokacin da ake ganin harkar rubutun lattattafan Hausa tana samun koma baya sakamakon yadda kasuwar littafin take durkushewa sai ga shi ana samun wasu masu kishin Hausa da ci gaban adabin suna iya ƙoƙarin su domin ganin harkar ba ta kai ga durkushewa ba.
Fatima Aminu Alhassan Kabo tana ɗaya daga cikin Mata  da suka tsaya tare da jajircewa wajen samar da Littattafai a wannan lokacin, bisa ƙoƙarin ta na samar da littafin da zai koyar tare da faɗakar da al’umma abin da ya shafi zamantakewar rayuwar aure musamman mata a wannan lokacin.
Don haka ne ta yi namijin ƙoƙari wajen samar da Littafin Sirrin Mace Musulma domin bayar da gudummawar ta ga al’umma.
A  ranar Asabar 17 ga Mayu ne dai aka yi taron  ƙaddamar da littafin na Sirrin Mace Musulma, wanda matashiyar marubuciyar Fatima Aminu Alhassan Kabo ta  wallafa
Taron, wanda aka gudanar da shi   a kofar fadar Hakimin Kabo,  da ke Karamar Hukumar Kabo a Jihar Kano, ya samu hakartar mahalartar manyan baki kama daga ‘yan siyasa da sarakuna Malaman Addini.
Tun da farko da yake dan takaitaccen bayani a wajen, Babban bako mai jawabi. Malam Ado Ahmad Gidan Dabino MON. Ya yaba wa marubuciyar bisa ƙoƙarin ta na samar da littafin wanda a ganin sa a wannan lokacin ba ƙaramin ƙoƙari ta yi ba.
Domin a cewar sa ” Rubutun lattattafai a yanzu sai wanda ya daure kuma ya yarda saɗaukarwa ne rubutun da ya yi domin bada gudummawar sa.
Don haka ya yi kira ga al’umma da su daure su sayi littafin domin amfanuwar su ga abubuwan da littafin ya kunsa.
Haka nan ya yi kira ga ‘yan siyasar yankin na Karamar Hukumar Kabo da ma na Jihar Kano baki ɗaya da su ɗauki nauyin wallafa littafin da yawa domin rabawa ga makarantu, don karuwar su da ilimin da ke cikin littafin.
Shi ma a nasa jawabin. Shugaban ƙaramar hukumar Kabo Hon. Lawal Najumen Kano, wanda shi ne babban mai ƙaddamarwa. Ya nuna farin cikin sa a game da samar da wannan littafin wanda kuma ya kasance marubuciyar ‘yar Karamar Hukumar sa ce ta Kabo, don haka ya ƙara jinjina a gare ta  tare  da ba ta kwarin gwiwa don ganin ta ci gaba da samar da Littattafai masu inganci don fadakar da al’umma
Inda kuma daga nan ya ƙaddamar da sayen kwafin littafin a kan naira miliyan ɗaya da rabi. Ya yin  da Karamar Hukumar Kabo ta saya a kan kuɗi Naira miliyan ɗaya.
Sai kuma masu rufa masa baya Wakilin Sanata Barau Jibril Wakilin Hakimin Kabo. Wakilin Hon. Nasiru Sule Garo. Wakilin Alhaji Fahad Adamu Dankabo, duk suka sayi nasu kwafin.
An dai tara kuɗi da kuma alkawurra masu yawa. Kuma Jama’a sun taru da dama a wajen.
Haka nan daga bangaren marubuta su ma taron ya samu halartar Malam Ado Ahmad Gidan Dabino MON, Sarkin Mawallafan Arewa tare da Sakataren kungiyar marubuta ta kasa (ANA) reshen jihar Kano Ibrahim Muhammad Indabawa, Malam Kabiru Yusuf Fagge (Anka) da kuma Malama Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo.

About The Author