September 18, 2026

Fagen Kimiyya: Ƙasan Duniya! Wata Halitta Mai Rai Da ake Kira Duniya (4)

GridArt_20250521_151251671

Fagen Kimiyya: Ƙasan Duniya! Wata Halitta Mai Rai Da ake Kira Duniya (4)

Duniya da muke rayuwa a kanta ba wai ta tsaya ne kawai a fadin da idonmu ke iya gani ba. Akwai wata duniya dabam, ko nace wata halitta mai rai a ƙarƙashin ƙafafunmu, mai cike da abubuwan ban mamaki, sirrika, da al’ajabi.

Idan muka tsaya da gaske muka yi ƙoƙarin fahimta, zamu gane cewa duniya ba dutse ba ce kawai ba, muna iya kiranta da wani jiki da ke ɗauke da zuciya, huhu, jijiya, da harma da numfashi kamar yadda mutum yake.

Lokacin da aka fara haƙo ƙasa daga saman fatar ta, zamu fara haɗuwa da yashi mai laushi, sai duwatsu masu sanyi, daga nan sai ruwa wanda ya ke ɓoye kuma a shimfiɗe ƙarƙashin ƙasar.

Amma yayin da aka ƙara yin ƙasa wajen haƙo ramin bayan an wuce ruwan, za’a taras da zafi, ana ƙara yin ƙasa zafin nan zai ci gaba da ƙaruwa har sai ya kai wani mataki mai tsananib firgitarwa.

Wannan nau’i na da za’a taras ba wai kamar na rana ba ne kawai, a’a, yana da tsananin zafi da ƙarfi fiye da yadda ran dan Adam zai iya jurewa. Wannan zai nuna mana cewa akwai wani abu a can ƙasan ƙasa da ke ƙonewa, yana narke duwatsu yana gina wani irin ruwa mai ban al’ajabi da ake kira ‘magma’ wato ruwan duwatsu mai tsananin zafi da ke shimfiɗe a ƙasa. Wannan shi ne ke tashi lokacin da aman wuta ke fashewa, yana bayyana mana fushin duniya ko wani sabon numfashi da take shaka.

Duniya tana da wata ganuwa da ke rarrabe jikinta kamar sassan jikin mutum. Samanta ita ake kira “litosphere”, inda muke takawa, muke gina gidaje, gonaki, da tituna.

Wannan shine fatar duniya. Amma a ƙarƙashinta akwai wani wuri da ake kira “mantle”, wani yanki ne da ke cike da zafi, kamar yadda kasko ke tafasa a wuta. A nan ne wasu farantai masu nauyi da faɗii suke shawagi kamar sunyi kama da ƙashin ƙugu, suna motsi a hankali. Wannan motsin da suke yi shine ke haddasa abubuwa kamar, girgizar ƙasa, aman wuta, da rushewar ƙasa.

Duniya tana motsawa ne ba tare da taimakon iska ba, amma za’a iya cewa da zafin zuciya irin motsin dake ɗauke da salo na ban mamakin da ba zamu iya misaltawa ba.

Wasu lokutta, girgizar ƙasa tana ne kamar ana jujjuya jiki, daga nan sai ta amsa da wani nau’in kukan (ƙara) da ake ji kamar ƙarar wuta da ke ƙoƙarin fitowa daga kasko. Wannan motsi yana da tasiri da ƙarfi fiye da duk wani motsin da muke gani a doron ƙasa.

Domin kuwa tsunami na iya tasowa, tekuna na iya birkicewa, da guguwa mai ƙarfi na iya lalata komai. Wannan yana nuna mana cewa duniya tana da rai da numfashi kuma tana yin canje-canje kamar yadda mutum ke sauya tunani ko motsi.

A cikin wannan numfashi na duniya, akwai wasu hanyoyi da suke da matuƙar zafi suna yawo ne kamar yadda jini ke zagayawa cikin jikin mutum. Waɗannan hanyoyi suna aikawa da wani nau’i na ƙarfi ko kuzari daga cikin duniya zuwa saman ta, sune ke taimakawa wajen girbin amfanin gona, sauyin yanayi, da kuma sarrafa iska da ruwan sama. Wannan kuzari ko ƙarfi shi ne ke tafiyar da damina, rani, da hatta yanda itatuwa ke yin fure da kuma bushewa.

Daga nan sai mu sauka zuwa mafi zurfin duniya inda ake samun core, da zamu iya kira da zuciyar duniya. Wannan wuri yana da bangarori biyu: core na waje (Outer core). Wannan wani ɓangare ne mai ɗauje da narkakkiyar ƙarfe musamman iron da nickel. Shi ke haifar da filin maganadisu na duniya, wanda ke kare mu daga hasken rana mai hatsari.

Kamar wata garkuwa ce da ba ta ganuwa, amma tana ceton duk abin da ke rayuwa. Sai kuma core na ciki (Inner Core) wanda aka ce yana da ƙarfi da zafi har ma yana iya zarce zafin rana. Zafin sa ya kai fiye da 5,500°C wato kimanin zafin rana!

Amma saboda ƙarancin motsi da karfi, wannan ɓangaren sam ba ya narkewa duk da tsananin zafin sa yana ci gaba da wanzuwa ne da aiki kamar ace zuciyar duniya, yana aiki ne cikin ƙwarewa, yana aiki kamar misalin injin da ke tafiyar da komai tun daga motsin farantai, zuwa motsin rana, da maganadisu da ke kare duniya daga hare-haren hasken rana mai cutarwa.

Wannan zuciya (Core) tana haifar da magnetic field, wato wata kariya mai ƙarfi da ke kewaye da duniya kamar garkuwa, tana kare mu daga hasken ultraviolet da sauran hasken da ke fitowa daga rana.

Idan da babu wannan kariya, to da ba zai yiwu mu rayu ba a duniya. Wannan kariyar da zai yiwu a ganta da a ido ba, amma kimiyya ta tabbatar da samuwarta kuma cikin ikon Allah tana nan tana kula da bamu kariya fiye da tunanin mu.

Idan muka sa lura sosai, zamu fahimci duniya kamar mutum ce da ke dauke da zuciya, jijiya, huhu, da numfashi. Ilimin kimiyya ya buɗe mana kofar fahimtar yanda tsarin duniya yake, tare da yanda take ci gaba wanzuwa da kuma tasirin ta ga halittun dake rayuwa a kanta, da irin kariyar da take basu daga halaka, lalle akwai abubuwan mamaki tare da lura game da wannan babbar halitta mai rai da muke kira da “Duniya) ko kuma “Earth” a turance.

A rubutun gaba, zan yi bayani a kan hanyoyin ruwa da iska, zamu kalli yadda ruwa ke zagayawa a cikin wannan halitta mai rai wato ‘Duniya’ kamar yadda jini ke yawo a jikin mutum.

Zamu fahimci yadda gajimare ke haɗuwa, da yanda ruwan sama ke sauka, da kuma yanda iska ke motsawa duk suna aiki tare da duniya kamar kamar dai gangar jikin mutum da sauran ɓangarorin sa.

About The Author