Sakon Ta’aziyya daga Lajnatul Hisbah Association of Nigeria Katsina State Command.
Sakon Ta’aziyya daga Lajnatul Hisbah Association of Nigeria Katsina State Command.
Babban Kwamadan Hisbah Alkali Malan Bulyaminu Muhammad Balarabe a madadin sa, iyalin sa da dukkannin ‘yan wannan runduna na kananan hukumomi 34 da ke fadin jihar Katsina maza da mata, Muna Miƙa sakon ta’aziyya zuwa ga Mai Girma Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa PhD da sauran duk iyalai ‘yan uwa da dangi da gwamnatin jihar da sauran duk al’ummar jihar Katsina baƙi ɗaya bisa ga wannan babban rashi da mu kayi na mahaifiya.
Lallai duk abinda Allah ya amsa nashi ne abinda ya bada shima nashi ne kuma komi Allah yasa masa lokacin da baya hucewa.
Amma Rashin Hajiya Safara’u Umaru Barebari babban rashi ne. Muna Rokon Allah da sunayen sa tsarkaka da siffofin sa maɗaukaka ya jikan ta ya yafe mata kurakuran ta, ya amshi bakwancin ta, ya haskaka makwancin ta ya ɗaukaka darajarta, ya bada ladar jinya, ya albarkaci zuri’arta ya bamu hakurin rashin ta, Amin ya gaffaru ya yahimu
Muhammad Aminu Bello
Sakatare na jaha a madadin shugaba
