Zamu Kawo Karshen Cuta Mai Karya Garkuwar jiki (SiDA) Nan Da Shekarar 2030 A Katsina – Dakta Bala Kankia
Shugaban hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki (SiDA) na jihar Katsina Dakta Bala Nuhu Kankia ya bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa na ganin an kauda cuta mai karya garkuwar jiki a jihar Katsina daga nan zuwa shekarar 2030.
Dakta Bala ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci gawatar hukumar zuwa babbar ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Katsina domin bayyana mata irin nasarorin da hukumar ta samu a ƙarƙashin gwamantin Malam Dikko Raɗɗa.
Ya ƙara da cewa, adadin masu cutar ya rago da kaso mai yawa, wanda ya ce suna fata za a cigaba da samun nasarar yaki da cutar har zuwa lokacin da za su tabbatar ta zama tarihi a jihar Katsina.
Dakta Bala ya yi ƙarin haske da cewa, akwai abubuwa guda uku da suka sanya gaba, wanda suke fatan samun nasara da kuma cigaba da nuna kulawa ga masu ɗauke da wannan lalura.
Shugaban hukumar ya jaddada cewa an samu gagarumar nasara wajen kawar da wannan cuta, inda ya bada misali da cewa yanzu kusan kashi 90% na masu ɗauke da wannan lalura sun san matsayin su, sannan an dora waɗanda suka san matsayin su akan magunguna ya ƙara da cewa idan kana shan magani ya zamana ka samu wani matsayi da zai hanaka yaɗa cutar a tsakanin al’umma.
“Duk nasarar da wannan hukuma ta samu, ta sameta a dalilin kulawa da gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa da kwamishinan harkokin kiwon lafiya Hon. Musa Adamu Funtua suke badawa duk lokacin da buƙatar hakan ta taso, saboda babu abinda za mu nema, mu rasa, sai dai godiya ga Allah ” inji shi
Kazalika shugaban hukumar ya yi bayanin cewa akwai manyan asibitoci 447 a fadin jihar Katsina inda ake yin bita da awo da bada magunguna sannan akwai ƙananan asibitoci guda 47 da su ake yi wa al’umma bita.
Da yake jawabi tun da farko kwamishinan kiwon lafiya na jihar Katsina Hon. Musa Adamu Funtua ya bayyana cewa a lokacin baya mutum mai ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki (SIDA) kamar wani dodo yake acikin al’umma amma yanzu an samu cigaba kowa ya fito fili har ana bukukuwa.
Hon. Musa Adamu Funtua ya ƙara da cewa wannan hukuma ta yi rawar gani wajen wayar da kan al’umma akan wannan cuta musamman irin shirye-shirye da taruruka da ake shiryawa domin Al’umma
A cewar sa, ana samun cigaba so sai a wannan yaƙi da ake cuta mai karya garkuwar jiki (SiDA) a jihar Katsina inda aka faɗaɗa shirin zuwa yankin ƙarkara.
“Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin Malam Dikko Umar Raɗɗa tana bada gudunmawa a wannan hukuma da duk wata hidama da ta shafi harkar kiwon lafiya a jihar domin cimma nasarar da ake buƙata” inji shi
Haka kuma Hon. Musa Adamu Funtua yana mai cewa babu wata hidama ta wannan hukuma da gwamnatin jihar Katsina bata sanya hannu ba, kuma yana bada tabbacin cewa duk abinda ya taso na hukumar yaƙi da cuta mai karya garkuwar jiki a shirye suke wajen ganin sun taimaka an samu nasara.
Kwamishinan ya yi kira ga shuwagabannin wannan hukuma da su cigaba da wayar da kan jama’a akan wannan lalura wanda ya ce hakan zai taimaka wajen rage ta da kuma kawo ƙarshen a nan gaba.
