Kungiyar Cigaban Garin Funtua Sun Yabawa Gwamna Raɗda Akan Faɗaɗa Tagwayen Hanyoyi.
Kungiyar cigaban garin Funtua mai suna Funtua Development Association sun yaba da ƙoƙarin gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa akan bada aikin tagwayen hanyoyin da suka ratsa cikin garin na Funtua
shugaban kungiyar Kwamarad Mannir Suleiman ya yi wannan yabon ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala wani taro da kungiyar ta yi a garin Funtua.
Kwamarad Mannir Suleiman shi ne tsohon shugaban kungiyar malaman kiwon lafiya ta jihar Katsina kuma mamba a kungiyar ta ƙasa ya nuna jin dadi da wannan aiki.
ya ƙara da cewa sake gina wadannan hanyoyi zai taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci a yanzu na Funtua baki daya
Aikin hanyoyin guda zai lashe kuɗi fiye da naira biliyan 20 wand ake sa ran kammalawa a cikin watanni sha takwas kamar yadda dan kwangilar ya yi alƙawari a lokacin kaddamar da aikin hanyar.
Alhaji Mannir Suleiman ya kuma yabawa gwamnan da sanata Muntari Dandutse bisa jajircewa da suka nuna wajan gina jami’ar kimiyya na gwamnatin tarayya a garin na Funtua.
Yace wannan mataki na bunƙasa harkar ilimi a jihar da sauƙaƙawa matasan yankin wasu halhalu na karatu .
Ya bayyana cewa duk da cewa wannan kungiyar bata daɗe da kafuwa ba kuma bata da haɗaka da siyasa amma zata goyi bayan duk wata gwamnati mai niyyar kawo cigaba a garin Funtua da jiha baki ɗaya
