September 17, 2026

Yanzu Ne Ya Kamata Matasa Su Mamaye Harkokin Siyasa –Shugaban NYCN Katsina

0

Daga Awwal Isah, Katsina

Majilisar matasa ta kasa reshen jihar Katsina (NYCN ta shirya wani taron tattaunawa da na addu’a kan goben matasa a wannan lokacin da ake kokarin barin baya a harkokin siyasa da na cigaba.

Taron wanda ya gudana a sakatariyarƙaramar hukumar Katsina, an shirya shi ne haɗin gwiwa da ɓangaren zartarwa dana majalissar dokoki.

Kuma ya na da nufin samar da haɗin gwiwa tsakanin ɓangaren zartarwa, dana majalissar dokoki, da kuma su kansu matasan don amfanin kowa.

Sauran abubuwan da taron ya maida ma hankali sun haɗa da sha’anin shugabanci da saka matasa a cikin shi, da rage matsalar fatara, da yaƙi da shan miyagun kwayoyi, da batun inganta tsaro da dai sauransu.

Tunda farko, saida shugaban majalissar matasan Shamsuddeen Ibrahim Shamo ya bayyana cewa, wannan shi ne lokacin da ya kamata matasa su mamaye muƙaman siyasa a ƙasar nan, inda kuma ya buƙace su da su guji aikata dukkan miyagun ayyuka.

A tsokacin shi, ɗan majalissar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina Hon. Ali Abu Albaba ya yaba ma majalissar matasan bisa shirya taron, sannan ya shawarce su da su ci gaba da bada gudunmuwar wurin ci gaban al’umma.

Ɗan majalissar dokokin ya kuma yi bayani akan shugabanci na-gari, da batun shigar matasa a cikin harkokin siyasa, da zama masu dogaro da kai, da yaƙi da shan miyagun kwayoyi, da dai sauransu.

An dai kammala taron ne da yi ma jahar Katsina, dama ƙasar nan addu’a don ganin sun samu tsaro.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *