Majalisar Makaman Katsina Ta Ce Za A Ba Shirin Bunƙasa Gandun Daji Fifiko.
Majalisar Makaman Katsina hakimin Bakori ta ce za a ba shirin bunƙasa gandun daji fifiko ta hanyar dasa itatuwa domin kiyaye muhallin a gundumar Makaman Katsina hakimin Alhaji Garba Tukur Idris Nadabo.
Ya bayyana hakan ne a Kurami lokacin ƙaddamar da gangamin wayar da kai da wata ƙungiya mai suna “Kurami Green Project” ta shiyar a garin Kurami da ke cikin gundumar.
Hakimin ya ce ana tsare-tsaren kafa wurin rainon itatuwa, inda za a riƙa rainon itatuwa masu bunƙasa tattalin arziki domin dasawa a garuruwan don samun ingantattar kariyar muhalli.
Alhaji Garba Tukur Idris Nadabo yayi nuni da cewa ofishin majalisar ya tuntuɓi ƙungiyar “Great Green World” a Abuja domin samar da itatuwan dasawa guda 50,000 da za a raba ga masu garin yankunan.
Makaman Katsina hakimin Bakori ya bayyana dasa itatuwa a matsayin babbar hanyar kiyaye muhalli daga zaizayar ƙasa, ɗumamar yanayi, ɓata muhalli da kuma samar da ingantaccen iska domin amfanin bil’adama.
Basaraken ya gode ma ƙungiyar “Kurami Green Project” bisa yin aikin, tare da buƙatar sauran ƙungiyoyi su kwaikwayi irin abinda ƙungiyar tayi.
A tsokacinshi, Walin Malama kuma uban ƙungiyar “Kurami Green Project” ya ce ƙungiyar ta samar itatuwa guda 2,000 domin dasawa a yankin mai garin Kurami.
Walin Makaman Alhaji Mohammed Tukur ya ce manufar gangamin wayar da kan akan dasa itatuwan da kungiyar ke yi shi ne don a bada gudunmawa wajen kare muhalli da bunƙasa sinadaran ƙasa, da dai sauransu.
Walin Makaman ya tabbatar ma da majalisar Makaman cewa, ƙungiyar zata samar da ƙarin itatuwan dasawa domin rabawa kyauta ga mutane.
Mai magarin Kurami Alhaji Bishir Aminu ya lissafo wasu shirye shirye da aka gudanar a Kurami a cikin watan azumi, inda aka ciyar da mutane masu ƙaramin ƙarfi.
Ya yaba ma hakimin bisa ziyartar yankin domin ƙaddamar da shirin.
Ya ja kunnen mutane su guji sare itatuwa ba kan ƙa’ida ba.
