Ƙwararru Akan Kula Da Muhalli Da Gandun Daji Sun Ja Kunnen Mutane Da Su Guji Sare Itatuwa.
Ƙwararru akan kula da muhalli da gandun daji sun ja kunnen mutane da su guji sare itatuwa.
Sun yi wannan kiran ne a lokacin wani taro da ƙunguyar Ideas and Global Academy haɗin gwiwa da sauran wasu ƙungiyoyi daban-daban suka shirya a akan sauyin yanayi kuma ya gudana a dakin taron Munaj da ke nan Katsina.
Dr. Musa Abdullahi Sufi daga wata gidauniya mai suna AAG da ke jihar Kano da Fatima Binta Suleiman da ke sashen nazarin sunadarai ta kwalejin koyarwa ta gwamnatin tarayya da ke nan Katsina sun shawarci mutane da su maida hankali ga shuka itatuwa domin kaucema ɗumamar yanayi.
Taron dai ya samu halartar wakilan hukumomi, ma’aikatu, ƙungiyoyi, wakilan ƙananan hukumomi, da dai sauransu.
Abubuwan da suka gudana a wurin taron sun haɗa da raba itatuwan da mutane zasu shuka, da sauransu
