Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Gwamna Dikko Raɗɗa Bashi Da Ɗan Takara Kuma Bai Turo Kowa ba. Cewar Gwajo-gwajo
Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Gwamna Dikko Raɗɗa Bashi Da Ɗan Takara Kuma Bai Turo Kowa ba. Cewar Gwajo-gwajo
Mai baiwa gwamnan jihar Katsina shawara akan harkokin siyasa Hon Yau Umar Gwajo-gwajo ya bayyana cewa gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa bashi da ɗan takara a zaɓen ƙananan hukumomin da ke tafe kuma bai turo kowa ba.
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da ya fitar aka rabawa manema labarai a Katsina
Hon. Ya’u Umar Gwajo-gwajo yace sun samu rahotanni yadda wasu Yan takarar ke cewa Gwamnan jihar Malam Dikko Umar Raɗɗa ne ya basu damar tsayawa takarar.
Dan haka ne Mai baiwa gwamnan shawara yace wannan ba gaskiya bane gwamnan Ya bada dama ga duk mai sha’awar tsayawa takara ya sai fom ya nemi jama’a.
Hon. Ya’u Umar Gwajo-gwajo yace Gwamnan jihar Malam Dikko Umar Radda mutum ne me mutunta demokradiyya dan haka kowanne ɗan jihar nada yancin tsayawa takara kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada madamar ya cika sharuɗan haka.
A don haka ne mai baiwa gwamnan shawara ke jan hankalin al’ummar jihar katsina da su sani gwamnan jihar bashi da ɗan takara na kowacce ƙaramar hukuma ko kansila
