September 18, 2026

Gwamnan Katsina Ya Ce Gudunmawar Da Za A Samu Ta Isa A Gina Hedkwatar Jam’iyar APC A Jihar.

0

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari yayi amannar cewa, gudunmawar da ake sa ran samu domin gina hedkwatar jam’iyar APC a jihar Katsina zata isa a kammala aikin.

Ya fadi hakan ne a wajen bikin tara kudin ginin hedkwatar jam’iyar akan hanyar Katsina Dutsinma.

Gwamnan ya yaba ma gudunmawar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari data dan takarar shugaban kasa na jam’iyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Ya kuma yaba ma tashi-fadin shugaban taron wanda ke zama ministan sufurin jiragen saman Najeriya sanata Hadi Sirika bisa ciyar da harkokin ma’aikatar shi gaba.

Shima ministan da yake magana, ya bukaci masu riƙe da ofisoshin siyasa, masu ayyukan taimakon al’umma, yan kasuwa, dama sauran ƴaƴan jam’iyar APC su bada gudunmawarsu domin ganin an kammala aikin.

Tunda farko da yake jawabin maraba, shugaban jam’iyar APC na jihar Katsina Sani Aliyu Daura ya ce jam’iyar na gudanar da al’amuran ta a cikin ginin haya sama da shekaru 8 da suka wuce.

Babban mai ƙaddamar da asusun tara kudin Architect Kabir Ibrahim Kebron ya sanar da bada gudunmawar naira miliyan 50 wanda ke zama ƙari ga miliyan 5 da ya bada.

Injiniyan dake aikin Muhammad Iliyasu ya ce an ƙiyasta cewa aikin zai lashe tsabar kuɗi naira biliyan 1.3.

Sauran da suka yi jawabi a wurin taron sun haɗa da shugaban jam’iyar APC na ƙasa Abdullahi Adamu, wanda ya samu wakilcin mai ba jam’iyar shawara ta fuskar shara’a na kasa Barrister Ahmed Usman El-Murzuq, mataimakin shugaban jam’iyar APC na jiha Bala Abu Musawa da kuma wakilan gwamnan jihar Zamfara.

Majiyarmu ta bada rohoton cewa, an tara miliyoyin nairori, inda Kabir Kebron ya bada mafi girman gudunmawar data kai ta naira miliyan 50.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *