AFAN Ta Jinjinawa Tinubu Bisa Naɗin Muhammad Abu Ibrahim Babban Sakataren Hukumar Noma da Samar da Kuɗaɗe Ta Ƙasa.
Kungiyar manoma ta ƙasa reshen jihar Katsina AFAN ta nuna godiyar ta ga shugaba Bola Ahmad Tinubu bisa nadin Muhammad Abu Ibrahim ɗan asalin Katsina a matsayin Baban Sakataren hukumar Noma da samar da Kudaɗai ta ƙasa
Haka yana kunshe ne acikin wata sanarwar da shugaban kungiyar Manoma Ta AFAN reshen jihar Katsina Hon. Yau Umar Gwajo-geajo ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai a Katsina
Kungiyar ta AFAN ta bayyana wannan muƙami a matsayin wanda aka ɗora kwarya a gurbin ta, saboda wanda aka naɗa ya cancanta kuma yana da kwarewar da zai yi aikin cikin nasara tare da kawo cigaba a sha’anin noma da kasuwanci a Nijeriya.
Haka kuma kungiyar ta jinjinawa shugaban ƙasa saboda irin kokarin da yake wajan naɗa matasa a cikin gwamnatin sa, wanda hakan ke nuna cika alƙawarin da ya ɗauka na tafiya da matasa a gwamnatin sa kamar ya yi faɗa a lokacin yakin neman zaɓe
Kungiyar manoma ta AFAN reshen jihar Katsina ta yi kira ga Muhammad Abu Ibrahim da kadda ya nuna gazawa, ya nuna shi ɗan ƙasa ne na gari daga jihar Katsina ta hanyar yin aiki tukuru domin cimma muradun ƙasa akan sha’anin noma da samar da kuɗaɗai
Haka kuma an yi kira ga ma’aikatan da sauran abokan aiki na Hukumomin gwamnati da su bashi goyon bayan da ake bukata domin samun nasarar aiki da ke gabansa.
Kazalika kungiyar a madadin mutanen jihar Katsina suna miƙa godiyar su ga shugaban ƙasa da gwamnatin sa sannan suna addu’ar Allah ya zaman lafiya a ƙasa baƙi ɗaya.
