September 18, 2026

Ranar Abinci Ta Duniya: Mata Sun Baje Kolin Abinda Suke Nomawa Da Sarafawa A Zamfara

0

Daga Hussaini Ibrahim

Uwargidan Gwamnan jihar Zamfara, Huriyya Dauda Lawal ,ta Jagoranci baje kolin abinda Mata suke nomawa da sarafawa a jihar.kuma ta dau alwashin tallafawa Mata Manoma da ke cikin Kananan hukumomi 14 da ke cikin Jihar.

Huriya Dauda ta bayyana haka ne a wajan bikin ranar abinci ta duniya da kungiyar mata manoma ta Kasa (NAWIA) reshen jihar Zamfara ta shirya a Gusau.

A Ranar 16 ga watan Oktoba ne ake bikin ranar abinci ta duniya a kowace shekara, an ware ranar ne domin wayar da kan jama’a kan mahimmancin abinci mai gina jiki, da kuma bayyana kalubalen da miliyoyin mutane ke fuskanta a fadin duniya saboda rashin samun abinci mai kyau.

Taken ranar abinci ta duniya na 2023 shine
“Samar da ruwa don inganta aikin gona”

Da take jawabi a wajan bikin , Huriyya ta ce, Miliyoyin mutane a duniya suna kokawa samun cin abinci ko da saua daya ne a rana, kuma dubbai suna mutuwa saboda yinwa.duk da karuwar samar da abinci a duniya, har yanzu akwai mutane da dama da ke fama da yinwa da rashin abinci mai gina jiki.

Gwamnatin jihar Zamfara, karkashin gwamna Dauda, na shirin bunkasa noma dan farfado da tattalin arzikin jihar ta bangaren noma da ada muke tinkaho da shi”.

A cewar uwargidan Gwamnan, gwamnatin jihar ta dukufa wajen ganin ta magance kalubalen da ake fuskanta na matsalar ruwa, dan inganta lafiya al’umar jihar.

Ta yi kira ga al’ummar jihar Zamfara musamman mata da su kara himma wajen yin noma,kuma ta bukaci jama’a da su kara yin addu’a domin kawo karshen matsalar rashin tsaro a jihar.

Haka zakalika ,Huriya ta zagaya rumfuna na kananan hukumomi goma sha hudu na jihar,da kowace ta baje kokolin abunda mata suke nomawa da kuma sarafawa da kansu .

Anan take Uwar gidan gwamnan ta basu tallafin na naira miliyan uku ga manoma mata na kananan hukumomin dan kara masu kwarin gyuwa wajan sana’ar noman.

Anasu jawabin Shugabar Shirin kungiyat Mata Manoma ta jihar Zamfara (NAWIA) Shema’u Nalada Da Sakatariyar Kungiyat,Hadiza Mahara,sun bayyana cewa, wannan shine karo na farko da kungiyar su ta baje kulin abunda suke nomawa,afadin jihar,kuma wannan kungiya tana da rasa a cikin Kananan hukumomi ,dan ganin Mata sun amfana da arzikin da Allah yayi mana na Kasar Noma.

Kuma wannan biki na yau ya kara tabbatar mana da cewa, gwamnatin jihar Zamfara tazo ne dan ta bunkasa harkar noma da kuma cigaban aluma.

Da fatan Allah ya dafa mata wajan samun masara ta baki daya Amin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *