September 17, 2026

Hon. Basiru Musa Ya Zamo Sabon Shugaban Karamar Hukumar Dandume

0

Daga Hussaini Yero

Saura watanin Shida wa’adin zababun Shugabanin Kananan Hukumomin Jihar Katsina ya kare ,sai gashi Basiru Musa ya zamo shugaban Karamar hukumar Dandume, Sakamakon gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa da ya ba Shugaban Karamar hukumar Dandume Hon Ya’u Nowa, Mukamin mai bashi shawara akan ayyukan da karin girma doka ta tabbatar da mataimakin sa ya maye gurbin shigaban ƙaramar hukumar ta Ɗandume.

Mataimakin Shugaban Karamar hukumar, Basiru Musa Dandume ne ya zamo Shugaba Karamar hukumar Dandume a yanzu haka.sai kuma Hon Abdullahi Takalmawa ya zama mataimakin Shugaban Karamar hukumar.

Mai Sharia a Kotun Majistiri da ke Funtua ne Samsudini Abdullah ya rantsar da su kamar yadda doka ta tanada.

A jawabin sa Shugaban mulki da kudi na Karamar hukumar Dandume,Alhaji Nura Suleman ‘Yan Daki yayi kira ga Ma’aikatan Karamar hukumar Dandume da su ba sabon Shugaban Karamar hukumar goyan baya dan samun nasarar ayyukan cigaba da Karamar hukumar ke kanyi a yanzu haka.

Babban bako a wajan rantsarwar ,shine Shugaban Hukumar Zabe Mai zaman kanta na Jihar Katsina,Ado Ladan, yayi kira ga sabon Shugaban Karamar da yayi aiki tsakanin da Allah kuma ya kula da mutane batare da banbanci Siyasa ba.dan samun nasarar ayyukan sa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *