September 18, 2026

Gwaman Zamfara Ya Maida Ma’aikatun Jihar daga 28 zuwa 16

0

Daga Hussaini Ibrahim

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya rattaba hannu akan rage ma’aikatun gwamnatin jihar daga 28 zuwa 16.dan Farfado da tattalin arzikin Jihar.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa ayau ranar Alhamis ta hannun mai magana da yawun gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris.

Suleman ,Ya ce gwamnan ya rattaba hannu kan dokar A yau ranar Alhamis a zauren majalisar da ke gidan gwamnati, Gusau.

Sabbin ma’aikatun da aka amince da su sune na ma’aikatar Noma, Kasafin Kudi da Kimiyya da Fasaha, Muhalli da Albarkatun Kasa, Kudi, Lafiya; da Kasuwanci,Ciniki da Masana’antu,

Sauran su ne Ma’aikatar Watsa Labarai da Gidaje da Ci gaban Birane da Ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu, Al’amuran Addini, Ma’aikatar Harkokin Mata da ta ayyuka da Matasa da Wasanni; Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida.

Kuma yanzu haka gwamna Dauda Lawal ya biya maaikata albashin wata biyu ga Ma’aikatan Jihar dan jindadin su da walwalar su.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *