November 17, 2026

Muhammad Adam Alkali irin Wakilin Da Jama’a su ke so ya Jagorance su

0

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A daidai lokacin da tsarin Dimokaradiyyar Kasar nan ya ke ƙara shekaru sai kuma jama’a suka himmatu da neman Jagorancin kishin ƙasa don cigaban ta da kuma kishin jama’a don ɗora Kasar a kan ilimi da wayewar zamani musamman a tsakanin matasa.

Haska hotun Ɗan Majalisa Mai wakiltar Jos ta Arewa Hon, Muhammad Adam Alkali a Majalisa da aka yi, yana Addu’a ya ja hankalin matasa tare da ba su sha’awa ganin sa matashi mai ilimin addini da kuma wayewar zamani.

Hon. Alkali dai nagartar ta sa ce ta sa aka zaɓe shi da kuma cantantar sa duk da ya fito a ƙaramar Jam’iyya, kuma a wannan karon ma da aka zo zaɓe jama’ar suka zaɓe shi a karo na biyu.

A satin da ya gabata lokacin da ‘yan majalisar wakilai suka yi zama domin murnar dawowar su bayan an kammala zaɓuɓuka an ga yadda Hon, Muhammad Adam Alkali ya ja addu’a cikin harshen Larabci da ya tabbatar da shi masanin harshen Larabci ne ba dan koyo ba.

Za a iya cewa shi ne Ɗan Majalisa na farko da muka fara gani a cikin Majalisa Wanda aka buɗe zaman da addu’a tare da Salatin Annabi Muhammad SAW kuma aka yi wa ƙasa addu’a.

Don haka mu a matsayin mu na ‘yan Arewa to irin wadannan su ne irin shugabannin da muke so. Saboda su na da sanin abin da ya shafi addini, da na zamani.

Saboda a yanzu abin da Kasar nan ta fi bukata shi ne addu’a, kuma ita kan ta rayuwar babu abin da zai ta yi tasiri sai da addu’a. Don haka irin yadda yadda ya kalli kasa a addu’ar sa sai ya nuna wannan su ne irin shugabannin da ya kamata a zaba.

“Mu a Nijeriya ƙasa ce ta addinai guda biyu, wato Muslunci da Kiristanci. To a ce dukkan mu haka muke da sanyya son ƙasa da yin aiki don ci gaban ta da kuma ƙoƙarin kiyaye dokokin addini”

To in muka samu shugabannin da suke da kishin ƙasa da al’ummar su irin wannan Allah zai taimaki su shugabannin, mu ma mabiyan sai Allah ya taimake mu.

Kuma kasanwar sa gwani a fagen karatun Alkur’ani Mahaddaci. A yanzu ma shi ne Garkuwan Kungiyar Hafizan Kur’ani. Don haka ta ko’ina muna buƙatar shugabanni irin waɗannan

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *