Hukumar DSS Ta Kama Masu Siyar Da Sabbin Kudin Naira.
Hukumar tsaron DSS ta cafke wasu masu sayar da sabbin takardun kudin naira a sassan kasar nan.
Ko da yake hukumar ta DSS ba ta bayyana sunaye da wuraren mutanen ba, hukumar a cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Litinin din 30/01/2023 ta ce wasu ma’aikatan bankunan yan kasuwa ne ke taimaka wa lamarin.
Sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar ta DSS, Dr. Peter Afunanya, ta yi gargadin cewa hukumar za ta bibiyi wadanda ke da hannu a cikin wannan aika-aika.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hukumar tsaron farin kayan ta sanar da jama’a cewa ta kama mutanen da ke da hannu wajen siyar da sabbin takardun kudin nairar da aka sake ma fasali. A yayin gudanar da ayyukansa sassan ƙasar nan, sun kuma tabbatar da cewa, wasu ma’aikatan bankin yan kasuwa ne ke taimakawa wajen tabarbarewar tattalin arziki, a cewar majiyar Popular News Hausa ta jaridar Vanguard.
