Masari Ya Kai Ziyarar Duba Aikin Daga Darajar Asibitin Kafur.
Gwamnan jihar Katsina ya kai ziyarar duba aikin daga darajar asibitin Kafur zuwa babbar asibiti.
Injiniyan dake kula da aikin Architech Maliki ne ya zagaya da gwamna Aminu Bello Masari a lokacin ziyarar domin duba aikin.
Da yake yima gwamnan jawabi, injiniyan dake kula da aikin ya ce yanzu haka ana zamanantarwa, ginawa da kuma daga darajar gine-ginen ta.
Abinda ya ce zai bata damar yin ayyuka kamar na manyan asibitoci.
Injiniyan ya ce an rushe muhimman gine-ginen asibitin, tare da samar da karin wuri domin fadada ta.
