Gwamna Masari Bawan Allah: Kana Barci Suna Yi Maka Munshari.
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
A wannan lokaci mai bala’in tsada a wajan ‘yan siyasa, lokaci ne da ke buƙatar tunani domin neman mafita irin ta siyasar 2023 da ke tafe da abubuwan ban mamaki, al’ajabi, tsoro da kuma firgici.
Duk ɗan siyasar da bai samu wanda zai taimaka masa a yanzu ba, to yana cikin wani irin hali na mutu kwaikwai rai kwaikwai, ma’ana ya zama abin tausayi a siyasa.
Tambayar anan ita ce, me ke sa ɗan siyasa ya rasa wanda zai taimake shi a lokacin da yake buƙatar hakan? Amsa ita ce abubuwan suna yawa.
Duk ɗan siyasar da ya kasa taimakon jama’a sai ya gamo da wancan matsala, duk ɗan siyasar da baya da tausayi zai haɗu da mugun ji da mugun gani amma a siyasa.
To amma abin cewa shi ne, gwamna Aminu Bello Masari yana da waɗancan halayyar da na ambata, idan amsa ita ce a’a to ya kamata ya ci arziki yawan alherinsa da kyautar sa da tausayin sa a siyasa da sauran al’amura.
Abubuwan da ke faruwa na rashin kyautatawa da wasu bara gurbi ke haddasawa a madadin gwamna Aminu Bello Masari ko gwamnatin sa na taimakawa wajan maida al’amura baya.
Misalin wannan batu nawa shi ne, yadda aka zargin wani hamshakin ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa sannan gashi SSA na gwamna Masari yana amfani da kusancin sa gwamna Aminu Bello Masari yana wani abu da ke kallon kamar yana ɓata masa suna.
A satin da ya gabata Alhaji Ɗahiru Mani ya ajiye aikinsa na gwamnati, kuma ya bayyanawa duniya cewa yana fuskantar barazana da tsangwama da kuma kokarin cin mutunci sa da ake shirin yi, shi yasa ya ajiye aikinsa.
Jin wannan magana daga bakin da baya karya, abinda zai zo wa jama’a shine ƙarƙashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari ake yi haka, kila ma wani ya ce shi yasa aka yin haka ko kuma yana sane haka ke faruwa amma bai ce komi ba.
Amma da tafiya ta yi tafiya sai ga zance ya fito, ashe wani ɗan siyasa ne ake zargin da kitsa wancan zargi da Ɗahiru Mani ya yi ta hanyar wani kwamishina kuma an ce ba Ɗahiru Mani bane kadai wancan mutumin ke shiryawa tuggu ba.
Wasu na ganin wannan al’amari dai yana cigaba da faruwa ba tare da sanin gwamna Aminu Bello Masari ba, sai daga baya ya sani, bayan da zance ya yi zance abu har ya kai kafar sadarwa ta intanet sannan ya ji abinda ke faruwa,.
Wata majiya ta ce gwamna Masari ya ce me yasa za a yi haka, inda har ya ce a kira kwamishinan ayi masa magana akan ɗaukarwa ‘yan adawa mataki irin na siyasa.
Abinda nake son jama’a su sani shi ne, irin haka na faruwa tuntuni amma kila shi gwamna Masari bai sani ba, kuma anki gaya masa, sai dai jama’a suna huce haushi irin wannan matakin ne akan shi gwamna da kuma gwamnatin sa.
Kadda in kaita da nisa, duk wannan abu yana faruwa ne sakamakon banbancin siyasa da aka samu tsakanin Ɗahiru Mani da wancan da ake zargi da kitsa wannan fitina.
Yanzu haka ance Hamisu Hara yana fuskantar irin wancan matsala da Ɗahiru Mani ya shiga har ya fita bayan ya ajiye aikinsa, kuma dai ana zargin wancan SSA ɗin da kitsa wannan al’amari duk da cewa bai fito fili ya bayyana cewa shi ne ke wannan aika aika ba.
Haka kuma wasu ma su bin al’amarin yau da kullum suna da ra’ayin cewa bai kamata ma’aikatan gwamnati su rika ɗaukar al’amarin siyasa fiye da aikin su ba, duk da cewa gwamnati ce ke amfana da abubuwan da suka yi a baya, kafin daga bisani ruwa ya yi tsami.
A irin wannan yanayi gwamna Aminu Bello Masari dai ya shafa faɗa cewa gwamnatin sa baza takurawa ‘yan adawa ba, harma ya ƙara da cewa zai ba su dama su rika baje kolin su, domin ta haka ne gwamnatinsa za ta iya gano wasu kurakuran da za su gyara cikin sauki.
To idan haka ne, shin gwamna Aminu Bello Masari ya san irin wannan taɓargaza na faruwa da yaran tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Inuwa irin su shi Ɗahiru Mani da Hamisu Hara waɗanda a baya sun kare gwamnatiin sa, yanzu sun canza sheƙa?
Idan har gwamna Aminu Bello Masari bai sani ba, to ya zama ke nan, yana barci su o’o suna yi masa munshari. Allah ya kyauta.
