September 18, 2026

Kungiyar Fataken Shanu Tayi Sabbin Shugabanni a Zamfara

0

Daga Hussaini Ibrahim

A jiya Labara ne , Kungiyar Fataken Shanu ta Jihar Zamfara,tayi zaben Shugabanninta ,bayan karewar wa’adin tsafin Shugabannin da suka kwashe shekaru hudo suna tafiyar da Kungiyar.

Shugaban zaben Shugaban ,Alhaji Abdullahi Abubakar ya bayyana cewa,kundin tsarin mulkin na Kungiyar ya aminta da yin zaben Sabin Shugabannin bayan wa’adin su ya kare na shekaru hudo.kuma kudin tsarin mulkin kungiyar ya bada zabi ,ko ayi zaben Shugabanni ko kuma ayi sasanci na fidda shugabannin inji Shugaban zaben Abdullahi Abubakar.

” Shugaban zaben ya kara da cewa, Manbobin kungiyar sun aminta da yin sasanci dan fidda shugabannin Kungiyar ta hanyar cancanta da kuma dataku ya sanya suka fidda shagabannin da zasu jagoranci Kungiyar na tsawon shekaru hudo cikin jihar ta Zamfara.Inji Shugaban.

“Abdullahi Abubakar ya bayyana, Alhaji Aminu Garba, Sarkin Fataken Shanu Masarauta Gusau,a Matsayin Shugaban Kungiyar ,sai Bashir Abubakar a Matsayin Sakatare ,sai Alhaji Sani Madur a Matsayin Ma’ajin Kungiyar,da kuma sauran Shugabannin goma sha takwas masu mukamai a Kungiyar ta Fataken Shanu.

Uba a wajan shine Mai Martaba ,Sarkin Katsinan Gusau Alhaji Ibrahim Bello ,ya bayyana jindadinsa ganin yadda ‘yan Kungiyar suka gabatar da zaben Sabin Shgabannin cikin kwanciyar hankali da lumana.kuma yayi kira a gare su da su rike amanar Manbobin kungiyar Kuma su ciyar da Kungiyar gaba akan yada suka samaita.kuma suji tsaron Allah wajan tafiyar da ayyukan Kungiyar dan samun nasara sana’ar su.

Babban baki a wajan zaben Sabin Shgabannin ,shine Gwamna Bello Matawallen Maradun da ya samu wakilcin ,Kwamishinan Matasa ,Hon Abdullahi Sifiro ya bayyana cewa, Kungiyar Fataken Shanu ta Jihar Zamfara,na daya daga cikin kungiyar da Jihar ke alfahari da ita wajan samar da kudin harajin a jihar dan itace tayi zara wajan biyan kudin haraji a fadin jihar .inj Gwamna Bello Matawallen.

“Gwamna Matawale ya kuma tabbatar da cewa, gwamnati zatayi iyaka kokari wajan kare mutunci Manbobin kungiyar a duk inda suka kai Shanu a fadin kasar nan.

Kuma a karshe yayi kira ga Sabin Shgabannin Kungiyar da su ji tsaron Allah wajan tafiyar da Kungiyar da kuma yaki da gurbatatun masu sayan Shanu ta barauniyar hanya .watau ta bayan fage ba cikin kungiyar ba.

Shima anasa jawabin sabon Shugaban Kungiyar na Jihar Zamfara,Aminu Garba Sarkin Fataken Shanu Masarauta Gusau,ya tabbatar da cewa,zasu rike wannan Kungiyar bisa amana da kuma aiki da Jami’an tsaro dan ganin an tsaftace Sana’ar da kuma kama masu saida shanun sata a cikin jihar.inji Shugaban Kungiyar, Aminu Garba Sarkin Fataken Shanu Masarauta Gusau.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *