September 16, 2026

Alhaji Zilkifilu Sani Ya Kuɓuta Daga Hannun Kidinafas A Katsina.

0

Rahotanni daga Iyalan ɗan kasuwar nan Alhaji Zilkifilu Sani wanda masu garkuwa da mutane suka sace akan hanyar Batsari sati Uku da suka wuce ya kuɓuta.

Majiyar Popular News Hausa ta bayyana cewa da farko an kaiwa ‘yan bindigar kudi har naira miliyan biyu amma suka ki sakinsa saboda a cewar su kuɗin sun yi kaɗan.

Mai ba mu labarin ya ce, bayan kamar mako guda da kai masu kuɗin farko, iyalansa dai suka sake shiga suka fita, aka ƙara tattara kimanin naira dubu dari biyar da wani abu aka sake kai mu sa.

‘”Cikin ikon Allah da taimakon Allah da kuma addu’oi da sadaka Allah ya kuɓutar da shi jiha Alhamis bayan shafe kusan kwana ashirin a hannun ‘yan bindigar” inji majiyar mu

Yanzu dai haka an garzaya da Alhaji Zilkifilu Sani zuwa asibiti domin duba lafiyar sa, sakamakon ɗauri da ciwowoka da ke jikinsa wanda ya samu a zamansa hannun ‘yan bindiga.

Sannan iyalansa suna ta miƙa godiya ga saura al’umma da suka taya su da addu’a da tausaya masu lokacin faruwar al’amarin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *