Zelensky Na Zargin Rasha Da Yunkurin Lalata Madatsar Ruwan Ukraine.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya zargi Rasha da yunkurin fasa wata madatsar ruwa domin mamaye wani babban yanki na Kherson da ke kudancin Ukraine a yayin da sojojinta suka janye daga kasar.
Kamar yadda majiyar Popular News Hausa ta Vanguard ta bayyana, Zelensky ya ce kasar abokiyar gaba ta yi niyyar yin hakan ne ta hanyar hakar tashar wutar lantarki ta Kakhovka daga yankin Kherson.
Ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ya yi da daddare a ranar Alhamis, inda ya ce lalata dam din zai yi illa ga kasar.
Zelensky ya ce, “lalata madatsar ruwan babban bala’i ne. Idan Rasha na shirya irin wannan hare haren, yana nufin yan ta’adda na sane cewa ba zasu bar Kherson ba, da kudancin kasar da ya hadadaCrimea.”
Ya yi kira a dauki matakai don hana Rasha aikata wannan aiki da zai zama mai illa ga rayuwar bil’adama, kuma zai iya hana tashar makamin nukiliyar Zaporizhzia samun ruwan da take buƙata wajen sanyaya zafin da take fitar.
“Dole ne dukkan Turawa, shugabannin duniya, da dukkanin kungiyoyin kasa da kasa su bayyana wa ‘yan ta’addar cewa irin wannan harin ta’addanci a kan Kakhovka HPP zai kasance daidai da amfani da makamai masu linzami,” in ji shi.
