EFCC Ta Kama Mutane 2 Da Ake Zargin Masu Yin Jabun Kudi Ne.
Hukumar da ke bankado masu yima tattalin arzikin Najeriya zagon kasa Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa ta kama wasu mutane biyu da ake zargin masu jabun kudi ne; Johnson Olumoyegun da Tanko Abubakar, a Abuja.
An kama su ne a watan Oktoban 2022 a Kubwa da Area 3 Axis cikin Abuja, da dalar Amurka $270,000 na bogi.
Bugu da kari, Olumoyegun ya yi ma wani jami’in hukumar sojan, inda ya yi amfani da katin shaidar EFCC na bogi mai suna Solomon David, inji majiyar Popular News Hausa ta FRCN.
An kuma same shi da fasfo din kungiyar ECOWAS mai suna Isa Bello. Saboda haka mahukunta suka ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Kafafen yada labarai sun bayyana cewa, rundunar shiyyar Ibadan ta hukumar EFCC, ta samu nasarar yankewa wasu mutane shida masu damfara ta yanar gizo hukuncin dauri daban-daban.
Dukkansu sun amsa laifin da ake tuhumar su da su. Don haka lauyoyin da ke kare masu shigar da kara, Modupe Akinkoye, Abdulrasheed Suleiman, Mabas Mabur da Shamsuddeen Bashir, sun yi nazari kan gaskiyar lamarin tare da rokon kotuna ta hukunta wadanda ake tuhuma tare da yanke musu hukunci daidai da abinda suka yi.
Mai shari’a Oluremi Oguntoyinbo na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abeokuta, jihar Ogun ya yanke wa Adekunle hukuncin daurin shekara daya a gidan yari, yayin da mai shari’a Bayo Taiwo na babbar kotun jihar Ibadan ta jihar Oyo ya yanke wa Olawale da Aigbe hukuncin daurin watanni shida a gidan yari, yayin da aka yanke ma Michael hidimar al’umma ta wata biyu.
Mai shari’a Olusola Adetujoye na babbar kotun jihar Oyo da ke Ibadan ta yanke wa Babatunde hukuncin daurin watanni uku a gidan yari yayin da mai shari’a Uche Agomoh na babbar kotun tarayya da ke Ibadan a jihar Oyo ya yanke wa Damilola hukuncin daurin watanni shida a gidan yari.
