September 18, 2026

Gwamnatin Jihar Katsina Za Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 1 Kan Tsaro.

0

Gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta kashe sama da naira miliyan dubu 1 ga hukumomin tsaron jihar a kokarinta na yaki da matsalar tsaro.

Gwamna Aminu Bello Masari ya fadi hakan a lokacin bikin yaye jami’an sa-kai guda 600 wanda ya gudana a kwalejin horar da jami’an hukumar tsaron farin kaya wato Civil Defence da ke cikin jihar Katsina.

Gwamna Aminu Masari wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Katsina Muntari Lawal, ya kara da cewa gwamnatin jihar na kashe ɗunbin kudi wajen yaki da matsalar tsaron.

Kamar yadda ya ce, shigar da yan sa-kan cikin ayyukan yaƙi da matsalar tsaron na nuna cewa, gwamnatin ba za ta taɓa mika wuya ga yan ta’adda ba.

A jawabin marabarshi, mai ba gwamna shawara akan harkokin tsaron Ibrahim Ahmad Katsina ya ce gwamnatin jihar ta yanke shawarar shigar da yan sa-kan ne don su taimaka ma jami’an tsaro wurin yaki da ta’addanci, hadi da sauran laifuka.

Kamar yadda ya ce, jimillar yan sa-kai dubu 1,100 ne aka yaye yanzu daga cikin guda dubu 3 da gwamnati ta dauka.

Mai ba gwamnan shawara ya yi fatan ganin wannan kokarin ya kawo karshen ta’addanci a cikin jihar.

Ya yi amfani da damar wajen yaba ma hukumar Civil Defence da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyan baya da hadin kan da su ka bada don tabbatar da samun nasarar shirin bada horon.

A nashi bangaren, mataimakin kwamandan hukumar ta Civi Defence na kasa Babangida Abdullahi Dutsinma ya ce hakan ya nuna hangen nesan gwamnatin jihar Katsina a bangaren kula da tsaro.

Ya kuma yi fatan ganin yunkurin zai haifar da ɗa mai ido duba da yadda aka koya masu dubarun aiki daban-daban a lokacin horon.

Shima a nashi jawabin sarkin Katsina Abdulmumini kabir Usman, wanda ya samu wakilcin Madawakin Katsina Hamza Abubakar Duwan, ya yaba ma gwamnatin jihar Katsina bisa bullowa da shirin bada horon, tare da yin alkawarin bada cikakken goyan bayan sarakunan gargajiya wajen yaki da matsalar.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *