Dikko Raɗɗa Ya Yi Gaba Da Magoya Bayan Dr Mustapha Inuwa 1,900 A Garin Haihuwarsa
Ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC Dakta Dikko Umar Raɗɗa ya ci tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina Mustapha Inuwa da yaki a garin haihuwarsa wato Ɗanmusa.
Waɗannan kalamai sun fito ne daga bakin daraktan yaɗa labarai na yakin neman zaɓen Dikko Raɗɗa Ahmad Abdulkadir Bakori a wata sanarwa da ya fitar kwana ɗaya bayan dawowa daga yaƙin neman zaɓen a garin Ɗanmusa
Haka kuma sanarwar ta ce Dikko Umar Raɗɗa ya yi nasarar yin awon gaba da magoya bayan tsohon sakataren gwamnatin kimanin dubu ɗaya da ɗari tara a ƙaramar hukumar Ɗanmusa.
“Mutanen da suka bar tafiyar jami’yyar PDP
suka dawo APC sun zo ne karkarshin jagorancin ɗan siyasa, Alhaji Sani Abu Miinista kuma sun fito ne daga Mazaɓu goma sha ɗaya na ƙaramar hukumar Ɗanmusa” inji sanarwar
Sanarwar ta cigaba da cewa, Alhaji Sani Abu Miinista ya mallaka duk ofisoshin jami’yyar PDP ga ɗan takarar gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa a lokacin wannan ziyara ta sa.
