‘Yan Bindiga Sun Sace wani Basarake A Katsina
‘Yan bindiga sun yi awon gaba da mai garin Ummadau a kan hanyar sa ta zuwa tabar tawagar kamfen ɗin Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC.
Majiya mai tushe ta tabbatar wa jaridun katsina city news da taskar labarai faruwar wannan lamari
Sai dai majiyar tace, hanyar Ummadau bata da kyau ko kadan.kuma wasu daga cikin masu faɗa aji na ƙaramar hukumar a jam’iyyar APC sun bada shawarar a kauce ma wannan hanya
Kamar yadda mai ba mu labarin ya ce shugaban ƙaramar hukumar Safana shine ya kafe sai an bi ta wannan hanyar mai matuƙar hadari
Sannan ya umurci duk wani maigari da ya fito da jama’arrshi domin su tarɓi ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyar APC
Majiyarmu tace yanzu haka, ana can ofishin shugaban ‘yan sanda na shiyyar Dutsinma ana tattauna yadda za a biyo wa lamarin.
